Kotu ta bayar da belin Bala Muhammad kan miliayn 500

Bala Mohammed Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ana zargin sa da karbar naira miliyan 800 a matsayin cin hanci

Wata babbar kotu a birni tarayyar Najeriya Abuja, ta bayar da belin tsohun ministan birnin Bala Muhammad a ranar Juma'a.

Mai shari'a Abubakar Talba ne ya bayar da belin nasa kan kudi naira milliyan 500, da kuma mutane biyu da za su tsaya masa inda ko wanne su shi ma zai kasance ya mallaki wannan adadin.

Kotun ta ce dole mutanen da Bala Muhammad zai gabatar daya ya kasance Sanata ne a majalisar dattijan kasar daya kuma ya kasance darakta ne a wata ma'aikatar gwamnatin tarayya.

Ana kuma so ya kasance suna da kadarori a Abuja da nuna shaidar biyan haraji a shekara uku da ta gabata.

Kotun ta kuma bukaci tsohon Ministan ya mikawa kotun fasfo dinsa.

Ana zargin Bala Muhammad ne da karbar fiye da naira miliyan 800 a matsayin na goro a lokacin da yake ministan babban birnin, da kuma kin bayyana kadarorinsa.

A ranar Laraba ce kotun ta tura shi gidan yari na Kuje kafin a yanke hukunci kan belinsa.

Za a ci gaba da sauraron karar a ranar 4 ga watan Yulin 2017.

A watan Oktobar 2016 ne hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta kama tsohon ministan a Abuja.

Labarai masu alaka