Ebola ta sake ɓarkewa a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo

Ebola ta yi sanadin mutuwar mutum dubu 12 a shekara uku da ta gabata Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ebola ta yi sanadin mutuwar mutum dubu 12 a shekara uku da ta gabata

A ranar Juma'a ce Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ayyana ɓarkewar annobar cutar Ebola a arewa maso gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.

Cutar wadda ta bulla tun ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.

An samu allurar rigakafin cutar Ebola

Gurbatacciyar iska ta fi HIV da Ebola illa ga dan adam

Ebola ta bar baya da kura

Kwayar Ebola kan dade a jikin mutum

WHO ta ce barkewar annobar ta shafi wani yanki da ke surƙuƙin daji a gundumar Bas-Ule, da ke kan iyakar Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka.

An yi saurin shawo kan annobar cutar Ebola da ta barke a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo a shekarar 2014, wacce ta kashe mutum 49 a kiyasin da jami'ai suka fitar.

Fiye da mutum dubu goma sha biyu ne suka mutu a kasashen da cutar Ebola ta fi kamari a yammacin Afirka, wato Guinea, da Laberia da Saliyo da kuma Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo a shekara ukun da ta gabata.