An ƙwace makamai sama da 2,500 a makarantun Birtaniya

Ann Maguire Hakkin mallakar hoto Maguire family
Image caption Wani dalibi ya soke Ann Maguire , malama a wata makaranta dake leeds da wuka har lahira

Wani sharhi da kungiyar manema labarai ta yi na bayanai daga 'yan sanda 32 cikin 43 da ke Ingila da Wales, ya ce an gano makamai da suka hada da takobi da gatari da bindigogi 2,579 a cikin shekara biyu da ta gabata har zuwa Maris din shekarar 2017.

Shugaban 'yan sandan ya ce ana ci gaba da samun karuwa a yawan daliban da ke zuwa makaranta da wukake, kuma lamarin na matukar daga hankali.

Kusan makarantu 25,850 ne ake da su a Ingila da Wales.

Shugabannin makarantun sun ce lafiyar yara ce abin da suka fi bai wa muhimmanci kuma makarantun na aiki ne tare da 'yan sanda domin kare yaran da ke makarantun.

A shekarar 2016 zuwa 2017, an gano makamai 1,369 wanda hakan ke nufin karin kaso 20 cikin 100 a kan na alkaluman shekarar da ta gabata.

Kaso biyar cikin lamuran sun danganci wukake ko takobi.

Wasu makaman da aka kwace sun hada da a kalla bindigogi 26.

A ciki har da da makaman da ba a saba kwacewa ba kamarsu gwangwaneyen giya da karafuna da suka kai tsayin inci 15 da kulki.

An kuma kama a kalla yara 47 masu shekaru kasa da 10, shekarar da za a iya kare mutum idan har aka shigar da kararsa da makamai.

Sun hada da yara masu shekara biyar guda uku, an kama daya daga cikinsu da wuka yayin da aka kama daya kuma da wani makamin daban.

'Yan Metropolitan da na garin Manchester na daga cikin wadanda aka tuntunba a lokacin da aka gudanar da binciken.

Taimakon 'Yan sanda

Baban jami'in 'yan sanda, Alf Hitchcock, wanda ke shugabantar 'yan sandan Birtaniya da ke kula da laifukan wuka ya ce: "Daukar makami, ko ma wane iri ne a makarantu ba lamari ne da makaranta za ta duba ita kadai ba; a ko da yaushe 'yan sanda da wadanda suke aiki tare da su suna muradin yin aiki tare kuma su dauki matakin da ya dace."

Ya kara da cewa, "A baya-bayan nan an samu karuwa a yawan yara da ke dauke da makamai kuma abin damuwa ne".

Babban jami'in 'yan sandan ya ce, "Za mu shawo kan lamarin inda za mu saka ido kan masu daukar makaman ba bisa ka'ida ba, kuma za mu yi aiki da masu sayar da makaman domin su rage sayarwa yara wukake."

Image caption An samu karuwa a yawan yara dake yawo da makamai kuma abin damuwa ne.

"Kasancewar 'yan sanda a makarantu, ko da kuwa a matsayinsu na jami'an da ke gabatar da jawabi ko kuma tattaunawa ko kuma su hada gwiwa da makarantun domin kariya, yana taimaka mana wajen ilmantar da yara, kuma a yi musu bayanin dalilin da yasa yawo da makami ba bisa ka'ida bai dace ba."

Alkalumman na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro ke yi wa laifukan da suka danganci wuka dirar mikiya.

A farkon wannan watan, 'yan sandan yankunan London suka sanar cewa jami'ai za su yi aiki tare da makarantu domin fito da matsalolin da ka iya faruwa sakamakon yawo da wuka.

Labarai masu alaka