Tsofaffi sun yi arangama da 'yan sanda a Venezuela

Kasar Venezuala Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsofaffin dai sun ce tura ta kai bango a kasar mai fama da karin tabarbarewar tattalin arziki

Dubban tsofaffi ne a Venezuela suka fito zanga-zanga kan titinan birnin Caracas, da sauran biranen kasar don nuna adawa da gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.

Suna kuma nuna rashin jin dadinsu game da tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

'Yan sanda sun toshe duk wata damar shiga manyan hanyoyin birnin na Caracas, inda suke amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa taron masu zanga-zangar.

Masu zanga zangar sun rika kai naushi, kuma suka bukaci 'yan sanda su mutunta su

Kasar Venezuela na fuskantar matsalar karancin kayan buƙatun rayuwa da suka hada da magunguna da kayan aiki a asibitoci.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun rika fesa hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu zanga-zangar

Da dama dai na ganin tsofaffi a matsayin wadanda suka fi fuskantar matsaloli a bangaren kiwon lafiya.

Garin Merida dai ya saba da zanga zangar daliban jami'a., sai dai a wannan karon dandazon tsofaffi ne suka yi wani gangami zuwa ofishin babban mai gabatar da kara ranar Juma'a.

Tsofaffin a cike suke da damuwa

Wani tsoho ya bayyana damuwarsu da cewa: " Gwamnati na kashe mu ta hanyoyi uku.

Muna mutuwa saboda karancin abinci, muna mutuwa saboda karancin magunguna, kuma ana kashe mu a yayin zanga-zanga.''

Wata dattijuwa ma da ke dogara sanda ta shaida wa BBC cewa ba ta taba shiga wani gangami ba, a tsawon rayuwarta, amma yanzu ta ga lokaci ya yi na ta yi hakan.

Wata dattujuwa na rike da wani kwali da aka rubuta wata alama da ke cewa '' Yau nake cika shekaru 60, kuma a karon farko ba ni da isasshen abin more rayuwa.''

Florentino Montilba, mai shekaru 75, ya ce ya fito zanga-zangar ce saboda wannan ita ce mafita ta karshe da ta rage musu.''

" Idan bukatar hakan ta so, za mu mutu ne a bakin titin nan.''

Mutane akalla 39 ne aka hallaka tun bayan da zanga zangar da aka rika yi don nuna adawa da gwamnatin makonni shida da suka gabata.

Tashin hankalin dai ya kara ta'azzara ne bayan da kotun kolin kasar ta yi yunkurin karbe iko daga majalisar dokoki wadda 'yan adawa ke da rinjaye a ranar 29 ga watan Maris.

Labarai masu alaka