'Yan ƙunar baƙin wake sun tarwatsa kansu a Jami'ar Maiduguri

Jami'ar Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan harin kunar bakin waken sun hallaka a yayin da suke shirin kai harin

'Yan harin ƙunar bakin wake uku sun tarwatsa kansu da kansu a lokacin da suka yi kokarin kutsawa sashen ayyuka na jami'ar Maiduguri, jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Harin ya auku ne da tsakar daren Asabar, kuma hukumomi sun tabbatar da cewa wani mai gadi na cikin wadanda suka mutu sakamakon fashewar bama-baman.

Jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA da takwararta ta jihar Borno BOSEMA a Maiduguri sun kwashe gawawwakin.

Waɗannan hare-hare na zuwa ne a lokacin da birnin Maiduguri ke fuskantar ƙaruwar masu yunƙurin kai hare-haren ƙunar-baƙin-wake, bayan jami'an tsaron ƙasar sun ce sun yi nasarar fatattakar mayaƙan Boko haram daga dajin Sambisa.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai daga hukumomin tsaro da kuma na jami'ar Maiduguri game da wannan hari.

A ranar 26 ga watan Afrilu ma, wasu jerin hare-haren ƙunar-baƙin-wake sun kashe mutum biyar a birnin Maiduguri.

Wadanda suka mutu a hare-haren sun hada da 'yan ƙunar-baƙin-wake huɗu da kuma wani ɗan kato da gora, wato Civilian JTF.

Labarai masu alaka