Pele: Baje-kolin kayan tarihin Sarkin ƙwallon ƙafa

Pele's Shirt Hakkin mallakar hoto NATIONAL FOOTBALL MUSEUM
Image caption Jesin da Pele ya sanya a wasan Cin Kofin Duniya na farko da ya halarta a 1958 da Rasha

Za a baje-kolin jesin Brazil wadda mashahurin ɗan ƙwallon ƙafa, Pele ya sa a gasar Cin Kofin Duniyan da ya fara halarta, da kuma kambun da aka ba shi na Sarkin Ƙwallo.

Ta hanyar ayyukan fasihai da masu ɗaukar hotuna, za a yi amfani da zane da fitattun wasannin ƙwallon ƙafa da ya buga don nuna matakai daban-daban na rayuwar Pele.

Baje-kolin zai kuma ƙunshi wasu kayan tarihi da ba a taɓa ganinsu ba, ciki har da lambar da ya samu bayan lashe Gasar Cin Kofin Duniya a 1962.

A ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, za a buɗe baje-kolin a gidan adana kayan tarihi na Burtaniya da ke Manchester har zuwa ranar 4 ga watan Maris ɗin 2018.

Hakkin mallakar hoto KEYSTONE/GETTY
Image caption Pele yana ɗan shekara 17 ne ya ci lambar samun nasara a gasar Cin Kofin Duniya ta farko

Kayan tarihin sun ƙunshi jesin Brazil da ya sanya a wasan da ya buga na farko a gasar Cin Kofin Duniyar 1958 da Rasha, sai kuma lambar da ya samu ta Cin Kofin Duniya a 1962, da kambun da aka ba shi yayin karawarsu da Chile.

Akwai ma wata ƙwallo wadda ya samu sakamakon ukun da ya ciyo wa ƙungiyar New York Cosmos a 1970 da kuma wani fasfo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pele yayin fafatawa tsakanin Brazil da Czechoslovakia a gasar Cin Kofin Duniya ta 1970
Hakkin mallakar hoto NATIONAL FOOTBALL MUSEUM
Image caption An bai wa hamshaƙin ɗan ƙwallon kambun sarauta a fagen sana'arsa
Hakkin mallakar hoto NATIONAL FOOTBALL MUSEUM
Image caption Gidan tarihin ya yi wa mutum-mutumin Pele kwaskwarima saboda shagalin baje-kolin

Gidan adana kayan tarihi ya kuma yi wa wani ƙaton mutum-mutumin Pele ƙarin gashi don karrama wannan biki.

Daraktan riƙo na gidan tarihin, Kevin Haygarth, ya ce: "Muna son yin shagalin tunawa da Pele ta wata hanya da ta dace da ƙimar wannan gawurtacce kuma haziƙin ɗan ƙwallo, mu kuma ƙawata wajen da ƙayatattun hotuna a gefe guda da wasu muhimman kayan tarihi."

Labarai masu alaka