Kun san 'yan Chibok ɗin da suka ƙi yarda su koma gida?

Kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da mutum 20,000 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da mutum 20,000

Kungiyar Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo wanda a cikinsa ta nuna mata hudu da ta ce 'yan Chibok ne wadanda suka ki yarda su koma wurin iyayensu.

Bidiyon ya nuna matan sanye da bakaken kaya da niqabi, inda daya daga cikinsu, rike da bindiga, ta bayyana mubaya'arta ga kungiyar ta Boko Haram.

Yarinyar ta ce ta ƙi yarda ta koma wurin mahaifanta ne saboda sun ƙi shiga Musulinci.

Ta ce babu wanda yake takura musu su yi aure, kamar yadda ake cewa kungiyar Boko Haram na yi wa matan da ta kama.

Yarinyar ta yi kama da macen da ta yi magana a cikin bidiyon da ƙungiyar Boko Haram ta fitar a watan Agustan da ya gabata.

A wancan bidiyon, ta yi ƙorafin cewa jiragen yaƙin sojin Najeriya na kai wa 'yan matan Chibok da ke tsare hare-hare sannan ta roƙi gwamnatin ƙasar ta yi musayarsu da kwamandojin Boko Haram da ke hannunta.

Da ma dai gwamnatin Najeriya ta ce akwai 'yar Chibok din da ta ƙi yarda ta bar hannun 'yan Boko Haram a lokacin da aka yi musayar 82 daga cikinsu da wasu 'yan Boko Haram din da ke hannun gwamnati a makon jiya.

'Babu gudu babu ja da baya'

A cikin bidiyo na biyu da Boko Haram ta fitar ranar Juma'a, ta ce ba za ta daina yaƙar gwamnatin ƙasar ba.

A bidiyon, wanda a cikinsa aka nuna wasu mutum biyar da ƙungiyar ta ce su ne gwamnatin Najeriya ta saka inda ita kuma aka ba ta 'yan matan Chibok 82, ta yi barazanar kai hare-hare a Abuja, babban birnin ƙasar.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce Boko Haram ta fitar da bidiyon ne domin yin farfagandar da ta saba yi.

Sanarwar, wacce kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya aike wa maneman labarai, ta ce sojojin za su ci gaba da murkushe 'ya'yan kungiyar har sai sun ga bayansu.

A cewar Birgediya Janar Kukasheka, "Kamar yadda kuka gani [ a cikin bidiyon], mutumin da ke wannan kumfar baki na cikin wadanda suka ci gajiyar musayar da aka yi ta sakin 'yan matan Chibok 82, inda shi ma aka sake shi, kuma ba shi da wani kuzari na iya yin komai, don haka ku yi watsi da barazanar da ya yi."

Ya bukaci 'yan kasar su ci gaba da sanya idanu kan duk abubuwan da ke faruwa a kewayensu domin tabbatar da cewa wani mutum ma mugun nufi bai kai hare-hare ba, tana mai cewa za ta ci gaba da kare rayukan 'yan kasar.

Da ma dai wasu masu sharhi sun yi gargadin cewa yin musayar 'yan matan Chibok din da dakarun Boko Haram da aka tsare ka iya ta'azzara matsalar tsaro a kasar, ko da yake gwamnati ta sha cewa hakan ba shi da wata matsala.


Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption An kai 'yan matan asibiti kafin su tafi fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Akwai alamar gajiya a jikinsu

Yadda aka karɓo 'yan matan

Hakkin mallakar hoto Twitter/ICRC_Africa
Image caption Kungiyar agaji ta ICRC ce ta shiga tsakanin gwamnati da 'yan Boko Haram

Wata majiya mai kusanci da yadda yarjejeniyar ta faru ta shaida wa BBC:

An ga wasu motocin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross sun shiga jeji a kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Daga nan kuma jiragen yaki biyu da kuma sojoji ta kasa suka yi musu rakiya. Kuma an ga wasu mutum biyu fuskarsu a rufe.

Daga bisani ne aka dauki 'yan matan zuwa birnin Maiduguri, a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.