Ba za mu yi sulhu da gwamnati ba - Boko Haram

Abu Darda ya ce ba za su yi sulhu da gwamnati ba Hakkin mallakar hoto YouTube
Image caption Abu Darda ya ce ba za su yi sulhu da gwamnati ba

Mayakan Boko Haram din da gwamnatin Najeriya ta saka bayan kungiyar ta saki 'yan matan Chibok 82 sun ce ba za su yi sulhu da gwamnati ba suna masu cewa nan gaba kadan za su soma kai hare-hare a kasar.

Wani bidiyo da kungiyar ta fitar ranar ya nuna mayakan na Boko Haram hudu a cikin wani daji, inda daya daga cikinsu wanda ya bayyana kansa da suna Abu Darda ya sha ce ba za su taba yin sulhu da gwamnatin Najeriya ba.

A cewarsa, shi ne mutumin da aka kama a Gombe saboda ya tayar da bama-bamai, yana mai cewa yanzu ya koma dajin Sambisa shi da 'yan uwansa da aka saka inda suka hadu da sauran 'yan kungiyar.

Ya ce gwamnati ba za ta san kuskuren da ta yi na sakar kwamandojin Boko Haram biyar ba sai sun soma kai hare-hare.

Abu Darda ya ce "Mu babu ruwanmu da sulhu."

"Kuna karya kuna cewa kun karar da Sambisa. Karya kuke yi. Kwanan nan za ku ji tashin bam a cikin Abuja", in ji shi.

Sai dai a sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce Boko Haram ta fitar da bidiyon ne domin yin farfagandar da ta saba yi.

Sanarwar, wacce kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya aike wa maneman labarai, ta ce sojojin za su ci gaba da murkushe 'ya'yan kungiyar har sai sun ga bayansu.

A cewar Birgediya Janar Kukasheka, "Kamar yadda kuka gani [ a cikin bidiyon], mutumin da ke wannan kumfar baki na cikin wadanda suka ci gajiyar musayar da aka yi ta sakin 'yan matan Chibok 82, inda shi ma aka sake shi, kuma ba shi da wani kuzari na iya yin komai, don haka ku yi watsi da barazanar da ya yi."

Ya bukaci 'yan kasar su ci gaba da sanya idanu kan duk abubuwan da ke faruwa a kewayensu domin tabbatar da cewa wani mutum ma mugun nufi bai kai hare-hare ba, tana mai cewa za ta ci gaba da kare rayukan 'yan kasar.

Da ma dai wasu masu sharhi sun yi gargadin cewa yin musayar 'yan matan Chibok din da dakarun Boko Haram da aka tsare ka iya ta'azzara matsalar tsaro a kasar, ko da yake gwamnati ta sha cewa hakan ba shi da wata matsala.

Labarai masu alaka