Mun dakatar da binciken masarautar Kano — Muhyi

Muhyi Magaji
Image caption Shugaban hukumaryaki da cin hanci ta jihar Kano Muhyi Magaji

Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano a Najeriya ta ce ta dakatar da binciken facaka da kudin jama'a da take yi wa masarautar Kanon.

Shugaban hukumar Muhyi Magaji, ya shaida wa BBC cewa sun dakatar da binciken ne saboda majalisar dokokin jihar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

Alhaji Magaji ya ce hukumar su ba da ta hurumi na gudanar da bincike a kan duk wani al'amari da ke gaban hukumar yaki da cin hanci ta EECC ko majalisar dokoki, ko kuma kotu.

A watan da ya gabata ne hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta ce ta bude bincike kan zargin facaka da kudin masarautar Kano sakamakon wasu korafe-korafe da ta samu daga jama'ar gari.

Sai dai a makon da ya gabata, Majalisar Dokoki ta jihar, ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan makamantan wadannan zarge-zarge.

Ta kuma bai wa kwamitin mako biyu domin ya gabatar da rahotonsa.

Sai dai tuni fadar Sarkin ta musanta zarge-zargen cewa ta kashe kudade ba bisa ka'ida ba, inda ta ce a shirye take ta bayar da hadin kai game da binciken da hukumomi suke yi.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Mai martaba Srkin Kano Muhammadu Sanusi II

A can baya din, Walin Kano Mahe Bashir Wali, ya ce babu abin da aka aikata da ya saba wa ka'ida.

Ya kuma gabatar da wasu takardu da ya ce suna nuna yadda fadar ta kashe kudaden da ake magana a kai dalla-dalla kamar yadda doka ta tanada.

Wasu masu sharhi na ganin wannan mataki na iya sanya shakku kan binciken da hukumomi suka kaddamar kan fadar, wanda dama wasu ke ganin na da alaka da siyasa.

Sai dai hukumomin sun sha musanta hakan.

Binciken aka kaddamar dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wasu kalamai da wasu ke ganin ba su yi wa mahukuntan jihar da ma kasa baki daya dadi ba.