'Na fi son harbewa da a yi min allurar mutuwa'

Ledford Hakkin mallakar hoto GeORGIA DEPARTMENT OF CORRECTIONS
Image caption A watan Janairun 1992 ne Ledford ya daɓa wa maƙwabcinsa ɗan shekara 73 wuƙar da ta zama ajalinsa

Wani ɗaurarre da ke jiran a zartar masa da hukuncin kisa a jihar Georgia ta Amurka ya nemi a yi masa haddi ta hanyar bindigewa kan hujjar cewa allurar mutuwar da ake yi, za ta yi masa ciwo matuƙa.

J W Ledford Jr yana shan magani saboda ciwon tsikokin jiki abin da lauyansa ya ce ka iya shafar zubin sinadaran ƙwaƙwalwa, ya kuma sanya shi "ciwon da bai saba ji ba".

An yanke wa Ledford hukunci kan kisan gillar da ya aikata na wani maƙwabcinsa a shekara ta 1992.

Wani alƙali ya kori shari'arsa a ranar Juma'a, sai dai lauyoyi sun ce za su ɗaukaka ƙara. Ranar Talata ce aka tsara za a zartar wa ɗaurarren hukunci.

Lauyoyin sun faɗa a cikin takardun kotu cewa Ledford yana shan maganin gabapentin tsawon kimanin shekara goma.

Sun ba da misali da bahasin ƙwararru cewa shan maganin gabapentin tsawon lokaci na jirkita ƙwaƙwalwa ta hanyar da sinadarin allurar mutuwa pentobarbital ba lallai ne ya iya sumar da mutum ba ko kuma ya hana jin wani abu.

"Akwai kasadar cewa Mr Ledford zai iya kasancewa a farke kuma cikin tsananin ciwo a lokacin da sinadaran pentobarbital ya kama kafofin numfashinsa, ya illata ƙwaƙwalwarsa da zuciya da huhunsa, yawu kuma ya ɗauke a bakinsa," a cewar takardun kotu.

Suka ce hakan zai keta 'yancin wanda za a kashe, a ƙarƙashin tanadi na takwas na tsarin mulkin Amurka, wanda ya hana "hukuncin ba-sabon-ba mai cike da ƙeta".

Kotun Ƙolin Amurka ta buƙaci cewa ana iya amfani da wata hanya ta daban don zartar da hukuncin kisa.

Ledford ka iya fuskantar matsala don kuwa jiha uku ce kawai a Amurka - Mississippi, Oklahoma and Utah - ke bari a zartar da hukuncin kisa ta hanyar bindigewa maimakon yin allurar mutuwa.

Dokar jihar Georgia ba ta ba da damar wannan zaɓi. Haka kuma babu wasu nau'o'in alluran mutuwa a yanzu don kuwa masana'antu haɗa magunguna da dama sun haramta yin amfani da magungunansu wajen zartar da hukuncin kisa.

Lauyoyin jihar Georgia sun ce "babu wata kasadar" fuskantar matsanancin ciwo kuma sun ƙalubalanci lokacin da aka yi amfani da shi wajen shigar da ƙara.

"Mai ƙarar ya bari sai ranar jajiberen zartar masa da hukunci kwatsam ya zo yana iƙirarin cewa ana ba shi maganin da zai iya yin tasiri kan haddin da za a zartar masa," suka ce a cikin takardun kotu.

"Idan mai ƙara da gaske yana ganin zaɓin fuskantar hukunci ta hanyar bindigewa ya fiye masa, ai da sai ya ankarar da gwamnati tun shekarun baya, maimakon kwana biyar kafin zartar masa da hukunci."

Labarai masu alaka