Fira ministan Canada ya je ofis da ƙaramin ɗansa

Hadrien Trudeau Hakkin mallakar hoto JUSTIN TRUDEAU
Image caption Hadrien Trudeau zaune a kan kujerar mulki ta mahaifinsa fira ministan Kanada

Fira ministan Kanada kuma sha-lelen intanet Justin Trudeau ya nuna wa sauran shugabannin duniya yadda ake jan hankalin mutane - ta hanyar zuwa ofishinsa da ɗansa mai shekara uku.

Harkokin fira ministan dai ba su tsaya ba, aikace-aikacensa a hukumance tsawon wannan yini sun haɗar da taro da rukunin 'yan jam'iyyarsa na ƙasa da fuskantar tambayoyi daga majalisar dattijai da kuma ganawa da shugabannin jami'a.

Duk da haka, ya samu lokacin yin wasan 'yar-ɓuya da ɗan nasa.

Hakkin mallakar hoto JUSTIN TRUDEAU
Image caption Justin Trudeau da ɗansa Hadrien na wasan 'yar ɓuya a ofishinsa na fira minista

Shi dai Hadrien Trudeau ya yi ta wasanni da tsalle-tsallensa ne a ofishin mahaifin kuma a hotunan da aka buga ta kafar sada zumunta yaron ne ya cinye.

An kuma ɗauki hotunan fira ministan da ɗansa a lokacin zantawa da 'yan jarida da 'yan siyasa.

Hakkin mallakar hoto JUSTIN TRUDEAU
Image caption Fira minista Justin Trudeau da ɗansa a taron manema labarai

Wani mai sharhi a Facebook ya ce "Abin sha'awa ... Da wayona lokacin da na ga hotunanka da na mahaifinka (tsohon Fira minista Pierre Trudeau) kana ɗan ƙarami."

Wani kuma ya ce "ko dai hakan na da kyau ga yunƙurinsa na son a sani ko a'a, babu dai wata kalma da za ka kira Mista Trudeau sai mai ƙaunar iyalinsa."

Hakkin mallakar hoto JUSTIN TRUDEAU
Image caption Hadrien Trudeau na ɗaga wa jama'a hannu a lokacin da suke taro da mahaifinsa

Tabbas, ba wannan ne karon farko da ɗan siyasar mai shekara 45 ya ja hankalin al'ummar duniya ba.

Magoya bayansa sun yaba wa ɗan siyasar mai sassaucin ra'ayi saboda nuna goyon bayansa ga 'yan gudun hijirar Syria da shiga macin masu auren jinsi kuma a fili ya bayyana kansa da cewa shi Na-mata ne.

Hakkin mallakar hoto JUSTIN TRUDEAU
Image caption Justin Trudeau da ɗansa Hadrien suna sassarfa a cikin fadar fira ministan

A makon jiya ma, wasu 'yan gudun hijirar Syria a Kanada suka sanya wa ɗansu sunansa.

Labarai masu alaka