Chelsea za ta ci gaba da inganta wasanta - Conte

Cesc Fabregas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zabi Cesc Fabregas a matsayin dan wasan da ya fi wasa mai kayatarwa

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce kungiyar za ta iya inganta wasanta bayan nasarar da suka yi na lashe kofin Premier na Ingila na bana kuma za ta yi kokarin rike gwanayen 'yan wasanta.

Chelsea ta dauki kofin na Premier karo na shida ne bayan ta doke West Brom da ci 1-0 ranar Juma'a.

Ana ta rade-radin cewa Conte, mai shekara 47, zai koma Inter Milan, yayin da wasu ke hasashen cewa mai yiwuwa 'yan wasa Diego Costa da Eden Hazard ka iya barin kungiyar.

Sai dai Conte ya ce, "Idan har za mu iya ci gaba da yin wasa da wadannan 'yan kwallon za mu iya inganta wasanmu sosai."

Tsohon kocin Juventus da Italiya ya jagoranci Chelsea, wacce ta gama kakar wasan bara a matsayi na 10, wajen daukar kofinsa na farko a kungiyar.

Rahotanni daga Italiya na cewa kungiyar kwallon kafar China a matakin Seria A club Inter na shirin biyan Conte £250,000 a duk mako idan ya bar Stamford Bridge.

Sai dai kocin ya ce shi da 'yan wasansa "yanzu ma muka soma wasa".

"Yanzu 'yan wasan sun san abubuwan da nake so, ni kuma na san halayensu, don haka za mu inganta wasanmu," in ji shi.

Ana hasashen cewa dan kasar Belgium Hazard, mai shekara 26, zai koma Real Madrid, yayin da shi kuma dan wasan gaba dan kasar Spain Costa, mai shekara 28, ake cewa zai koma wata kungiya a China.

Amma Conte ya ce, "Wannan kungiyar na son fafatawa a dukkan gasar da za a yi nan gaba domin lashe ta - burinmu daya ne".

Labarai masu alaka