Me Afirka za ta amfana da shi a mulkin Macron?

france Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fara aiki

Yayin da sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fara aiki, al'ummomin Afirka za su zura ido su ga yadda zai cika wasu alkawura da yayi wa nahiyar a lokacin da yake yakin neman zabe.

Macron mai sassaucin ra'ayi da ke goyon bayan haɗin kan Turai ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arziƙin Faransa da yi wa tsohon tsarin siyasar ƙasar garambawul.

Sai dai ba Faransa kadai ya yi alkawarin kawo wa sauyi ba, har ma da kasashen Afirka. Wasu daga cikin alkawuran da yayi wa Afirka sun hada da:

Yaki da masu tsattsaurar akidar Islama

Daga cikin 'yan alkawuran da Mista Macron ya yi game da Afirka, yaki da masu tayar da kayar baya, masu tsattsaurar akidar Islama na gaba-gaba a cikin manufofinsa ga nahiyar.

An zabe shi ne a daidai lokacin da Faransa ke cikin dokar ta baci saboda jerin hare-haren na masu tsattsaurar akidar Islama.

A lokacin yakin neman zaben shi, ya ce ba Faransa ce kadai kasar da ke fama da matsalar ta'addanci ba, Afirka ma na fama da matsalar, inda yayi nuni da abubuwan dake faruwa a Mali, da Burkina Faso da Ivory Coast da sauran kasashe.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Faransa ta girke sojoji dubu hudu dake yaki da ta'addanci a Afirka

Sabon shugaban Faransar ba shi da niyyar janye sojojin kasar dubu hudu da suke yaki da ta'addanci a wasu kasashen Afirka

Bayar da agaji, da habbaka kasuwanci da kawo ci gaba

An zabi Mista Macron ne domin kare muradun Faransa a ko ina a duniya, kuma zai tabbatar da hakan a dangantakarshi da nahiyar Afirka.

Wani mai sharhi kan sha'anin siyasa, Serge Theophile Balima ya shaidawa BBC cewa Mista Macron mutun ne da yayi imani da kasuwanci, kuma zai yi duk mai yiwuwa domin fadada kasuwanci tsakanin Faransa da Afirka.

Ya sha alwashin cewa zai matsawa kungiyar kasashe ashirin mafiya karfin tattalin arziki- G20, da za su yi taro a watan Yuli a Jamus, wajen ganin sun goyi bayan bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabon shugaban Faransa zai bullo da sabbin hanyoyin cinikayya da Afirka

Ya kuma yi alkawarin ba Afirka akasarin kudaden tallafi da Faransa ke ba kasashen duniya.