Ivory Coast: Sojoji na yunƙurin kwantar da bore

Kasar Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojoji masu bore sun karbe ikon birnin Boauke, na biyu mafi girma a kasar ta Ivory Coast

Rundunar sojin Ivory Coast ta ce ta kaddamar da yunƙurin maido da doka da oda a birnin Bouake, na biyu mafi girma a kasar, wanda cikin kwana uku ya kasance karkashin ikon dakaru masu bore.

Sojojin sun fantsama kan tituna a birane da dama ranar Asabar, inda suka rufe hanyoyin shiga birnin Bouake har ma da rufe shaguna.

Suna boren ne a kan jinkirin da aka samu wajen biyansu kuɗaɗen alawus da gwamnati ta yi musu alkawari, bayan sun yi makamancin wannan bore a watan Janairu.

Sun kuma ce a shirye suke su yi fito na fito, muddin sojoji suka shiga cikin lamarin.

An jikata farar hula shida, lokacin da sojoji suka bude wuta kan masu zanga-zangar goyon bayan gwamnati a ranar Asabar.

Dakarun na kara dannawa

Wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi ta ce yunƙurin sojin ƙasar na nan tafe, babban hafsan sojin Ivory Coast Janar Sékou Touré ya ce akasarin sojoji masu boren sun saurari kiran da aka yi musu a baya na su janye.

Amma kuma ya ce wasu sojojin sun ci gaba da karya dokoki, abin da ya sa aka kaddamar da wannan atisaye.

A watan Janairu ne sojojin suka tilastawa gwamnati a kan ta biya su dala dubu 8 ko fam dubu shida da dari biyu kowannensu, a matsayin alwaus din da zai sa su kawo karshen boren.

A cikin wannan watan ne ya kamata suka karbi sauran kudaden nasu, kuma dubban masu boren sun fusata saboda rashin tuntubarsu a lokacin da wani mai magana da yawunsu a ranar Alhamis ya ce za su janye bukatun nasu.

Gwamnatin Ivory Cost din dai ta ce ba za ta sasanta da sojoji marasa da'a ba.

Tunzurin dai ya haifar da fargabar sake aukuwar tashin hankali da aka taba fuskanta lokacin yakin basasar kasar da aka shafe shekara goma ana gwabzawa, wanda ya kawo karashe a 2011.

Akasarin wadanda suka yi boren a cikin watan Janairu tsoffin 'yan tawaye ne da suka shiga aikin soja bayan da aka kawo karshen tashin hankalin.

Labarai masu alaka