Ebola: Nigeria na ɗaukar matakan riga-kafi

Cutar Ebola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cutar Ebola ta hallaka mutane da dama a wasu kasashen Afirka

Nijeriya ta ce ta fara ɗaukar matakan da suka dace a ƙoƙarinta na riga-kafin cutar Ebola, bayan samun ɓullarta a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo a baya-bayan nan.

Ƙasar dai na ɗaya daga cikin ƙasashen yankin Afirka ta yamma da suka yi fama da cutar Ebola a shekara ta 2014, lokacin da ƙwayar cutar ta harbi mutum 20 daga ciki kuma 9 suka mutu.

Ministan lafiya na Nijeriya, Farfesa Isaac Adewole ya ce ya ba da umarnin daukar matakan da suka dace don kare al'ummar ƙasar daga duk wata barazana da za a iya fuskanta nan gaba.

Matakan dai za su bayar da dukkan bayanan da mutane ke buƙatar sani game da cutar Ebola ta yadda za su iya farga da zarar wata alama ta bayyana da nufin sanar da hukumomi nan take.

Haka zalika, duk wasu alamu da aka gani game da cutar za a dauki mataki take-yanke na yin gwaji domin a hakikance lamarin.

Ma'aikatar lafiyar ta kuma yi kira ga al'ummar kasar su kwantar da hankula kuma kada su razana game da sake ɓullar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo da Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar.

Ta ce cibiyar kula ɓarkewar annoba ta Nijeriya na da kayan aiki da ma'aikata domin bai wa al'umma kariya.

Ta kuma buƙaci mutane da kada su yi wata-wata wajen sanar da duk wasu alamomi da za su gani na bayyane a tsakanin al'umma kan wannan cuta .

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Nijeriya ta ce kada hankalin 'yan kasar ya tashi game da barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo

Ma'aikatan lafiya za su binciki duk wani da ya nuna wasu alamomi na irin wanda ke dauke da cutar ta Ebola.

Alamun dai sun hada da zazzabi da gajiya da kasala da jiri da ciwon gabobi da kuma tsattsafowar jini daga fata ko ta baki da kunne.

A ranar 11 ga wannan wata ne Ministan lafiya na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya sanar da Hukumar Lafiya ta Duniya cewa wasu marasa lafiyan da aka bincika a kasar sun nuna alamun kwayoyin cutar Ebola.

Bayan wannan kuma sai reshen Afirka na Hukumar Lafiya ya ba da shelar cewa mutum tara sun kamu da cutar kuma uku daga cikinsu sun mutu a yankin Likati na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.

Labarai masu alaka