''Yan siyasa na sayar da filayen kiwonmu ga aminansu'

Ana yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya

A jihar Kano da ke arewa-maso-yammacin Najeriya, makiyaya na kuka da matakan da suke zargin wasu shugabannin kananan hukumomi ke dauka suna sayar da filayen kiwo da buratali ga aminai da magoya bayansu.

Makiyayan sun ce lamarin ka iya munana rikicin da ake samu tsakaninsu da manoma.

Ma`aikatar gona ta jihar Kano dai ta yi alwashin magance matsalar.

Wannan dai na faruwa ne a lokacin da gwamnatin jihar ke kokarin hada gwiwa da gwamnatin tarayya wajen samar da wuraren kiwo na zamani ga makiyaya.

Makiyayan, sun bayyana cewa ba su da gatan da ya wuce ragowar burtali da makiyayun da ke jihar Kano, saboda a nan ne suke yawace-yawacensu na kiwo.

Sun ce cinye musu filayen da suke zargin mahukunta a matakan kananan hukumomi ke yi, ya fara tilasta wa wasu makiyayan kaura zuwa nisan duniya don ciyar da dabbobinsu, inda su kan fada hadari mai yawa, ciki har da `yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane suna karbar kudin fansa.

Alhaji Ahmad Canji Mangari shi ne shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta gan Allah, reshen jihar Kano ya ce, "Makiyayun nan ba su ishe mu ba ma, maimakon mu samu kari daga wajen gwamnati, amma sai illa muke samu illa inda wasu shugabannin kanana hukumomin ke kwacewa."

Ya kara da cewa, "Don haka muna so gwamnati ta kwato mana wadannan filaye da burtalai namu don a samu raguwar fada tsakaninmu da manoma."

A karshen wannan watan Mayun ne dai wa'adin shugabannin kananan hukumomin jihar Kanon zai cika, kuma wannan ne ya sa ake zargin cewa wasunsu na warwaso ko wadakar karshe.

Bayanan hoto,

Gwamna Ganduje ya ce za a shawo kan matsalar

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko da a `yan kwanakin nan ma an zargi wasu shugabannin kananan hukumomin da ke Kanon da raba filayen makarantu don gina shaguna.

Na yi kokarin jin ta bakin ko da guda daga cikin shugaban kananan hukumomin ake zargi da raba filayen kiwon, ban yi nasara ba.

Amma ma`aikatar gonar jihar Kano, wadda ke da alhakin kula da filayen kiwo da burtalin, ta ce gwamnati na sane da wannan matsalar, har ma ta dauki mataki.

Alhaji Nasiru Gawuna shi ne Kwamishinan Noma na jihar ya ce, "Matakin da aka dauka shi ne, gwamna ya bada umarni cewa daga yanzu duk abin da za a aiwatar kan batun burtalai to sai ya biyo ta gaban gwamna, don haka makiyaya su kwantar da hankalinsu yanzu duk za a soke wadanda aka bayar din."

Wannan zargin kacancana filayen kiwon dai ana yin sa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta zabi wasu jihohi, ciki har da jihar Kano don hada-gwiwa wajen samar da makiyayu na zamani da nufin tsugunar da makiyaya, don inganta harkar kiwo da magance rikicinsu da manoma a Najeriyar baki daya.

Kuma idan wannan zargin ya tabbata, to zai iya zama babban koma-baya.