Hare-haren intanet; da sauran rina a kaba

Harin intanet din ya shafi kasashe 150 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harin intanet din ya shafi kasashe 150

Harin manhajar da ya shafi kasashe 150 ya fara raguwa, amma an sami rahotannin sabbin hare-hare daga nahiyar Asiya da Turai a ranar Litinin.

An yi kira ga ma'aikata da za su koma bakin aiki a ranar Litinin din, da su yi tsantseni wajen amfani da na'uraorin komfutarsu.

Wannan manhajar ta WannaCry ta fara bazuwa ne ranar Juma'a, inda take kulle na'urori masu kwakwalwa har sai an biya dalar Amurka 300.

Zuwa yanzu wannan harin ya shafi dubban daruruwan na'urori. Babban kamfanin manhaja na Microsoft ya ce wannan harin ya zama wani babban kalubale.

Wani binciken da BBC ta gabatar a kan asusun ajiya guda uku da wadanda suka saki manhajar suka ce a rika biyan kudaden fansar a cikin su, ya nuna cewa an biya dalar Amurka dubu 38 ne kawai (Fam 29,400) zuwa safiyar Litinin.

Amma saboda kashedin da masu manhajar fansar ta WannaCry suka yi na nunka kudin fansar bayan kwananki uku idan ba'a biya ba na iya sa a sami karuwar masu biyan kudin fansar.

Gargadin ya kara da cewa za'a share dukkan bayanan da ke cikin na'urar da ba ta biya kudaden ba cikin kwanaki bakwai.

Kamfanoni da ma'aikatun da wannann harin ya shafa sun hada da kamfanin jiragen kasa na Jamus watau Deutsche Bahn, da kamfanin sadarwa Telefonica na kasar Spaniya da babban kamfanin gidan waya na Amurka FedEx da ma'aikatar harkokin cikin gida na Rasha.

Yaya lamarin yake a ranar Litinin?

Cikin karshen mako, kamfanoni da dama sun yi hayar kwararru domin kare kansu daga sabbin hare-hare.

Da alama al'amarin ya fara sauki a nahiyar Turai.

Babban kakakin hukumar tsaron Turai ta Europol Jan Op Gen Oorth, ya sanar wa da kamfanin watsa labarai na Agence France-Presse cewa, "Mun ji dadin cewa yawan wadanda harin mahajar WannaCry ya shafa basu karu ba, kuma a nan Turai da alama mun shawo kan abubuwa, wannan ba karamar nasara ce ba."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin ya shafi wata tashar jirgin kasa ta Jamus

"Da alama ma'aikatan tsaro na yanar gizo sun yi abin da ya kamata, watau saka manhajar samar da kariya daga harin.

Kamfanin Renault mai yin motocin hawa yace ba zai bude masana'antarsa da ke garin Douai ba ranar Litinin har sai ya magance matsalar harin.

A Birtaniya, hukumar kiwon lafiya ta NHS ta ce bakwai daga cikin ma'aikatu 47 da aka kai wa hari a kasar har yanzu suna fama da matsaloli masu dama.

A nahiyar Asiya kuwa an sami rahotanni da suke nuna saukin hare-haren.

A Austireliya: Kamfanoni uku ne suka bayar da rahoton harin ya shafe su.

A Koriya ta Kudu: Rahotannin hare-hare tara kawai aka samu. Harin ya hana wani gidan silima nuna samfotin fina-finai.

A Indonisiya: Harin ya shafi bayanan marasa lafiya a asibiti guda daya ne kawai.

A Japan: Kamfanonin mota na Nissan da Hitachi sun ce wasu sassa kadan harin ya shafa.

A Sin: Da farko harin ya shafi dubban daruruwan na'urori, in ji kamfanin Qihoo na kasar Sin. Harin yafi shafar jami'o'i tun da sun fi amfani da tsofaffin na'urorin komfuta.

Akwai na'urori hada-hadar kudade da wasu ma'aikatun gwamnati da harin ya shafa, amma abin bai yi tsanani ba.

Harin bai shafi bankuna da ayyukan kasuwanci ba sosai.

Su waye suke da alhakin wannan hare-haren?

"Wannan harin ba zai dade ba. Babu wanda ya sani," In ji Jan Op Gen Oorth na hukumar Europol: "Da sauran lokaci kafin mu iya ganewa… amma muna kokarin samar da wata manhajar da zata bude na'urorin da harin ya shafa".

Ya kamata mutane su biya kudin fansar?

Kamfanoni a Asiya da Turai sun gargadi ma'aikatansu da su yi hattara wajen bude sakonnin Imel.

Sakon hukumar yaki da manyan laifuka ta Birtaniya shi ne "Kada a biya! " - domin babu tabbacin za a gyara barnar da aka yi.

Wani ma'aikacin kamfanin Network Box na Hong Kong ya fada ma Reuters cewa, akwai "sauran 'bama-bamai' masu yawa da ke boye a cikin Imel din jama'a", inda ya ce kamfaninsu ya gano wani sabon salon manhajar da ke boye a shafukan intanet da aka yi wa kutse.

Mene ne "ransomware"?

Becky Pinkard kwararriya ce a kamfanin Birtaniya mai samar da tsaro na intanet watau Digital Shadows, ta ce al'amarin na iya tabarbarewa, domin wadanda suka aika da manhajar, ko wasu masu son kwaikwayar su zasu iya sauya manhajar.

Wani mai binciken batutuwan tsaro a intanet mai suna, "MalwareTech" ya taimaka wajen dakile kaifin harin manhajar, ya ce akwai yiwuwar "samun wani hari… musamman a ranar Litinin".

Kafafen watsa labaran Birtaniya sun bayyana cewa Marcus Hutchins mai shekara 22 shi ne MalwareTech.

An lakaba masa sunan "gwarzon ba zata" bayan da ya yi rajistar wani shafin intanet don sa ido a kan yadda manhajar ke bazuwa a duniya, aikin da kuma ya yi sanadiyyar tsayar da harin baki daya.

Me yasa Microsoft yayi gargadin 'a farka'?

Babban kamfanin manhajar komfutan yace hukumar tsaron Amurka (NSA) ce ta kirkiri manhajar da aka kai hare-haren da ita, kuma wasu ne suka sace manhajar.

Kamfanin ya soki yadda gwamnatoci ke ajiye bayanan su ba tare da sun samar da kariya daga manhaja irin wannan ba.

Harin ya shafi wata tashar jirgin kasa a Chemnitz dake gabashin Jamus

Shugaban Microsoft Brad Smith wanda kuma shi ne babban lauyan kamfanin ya ce, "Mun ga yadda ake fallasa bayanan sirri na hukumar CIA a shafukan Wikileaks, kuma yanzu ga wannan manhajar da ta shafi abokan kasuwancinmu a ko'ina cikin duniya.

"Kwatankwacin wannan harin shi ne kamar wasu su sace bama-baman Tomahawk masu linzami na sojojin Amurka."

Kamfanin ya ce ma'aikatu da yawa sun gaza wajen samar da kariya ga na'urorinsu, dalilin da ya ba manhajar damar bazuwa.

Kamfanin Microsoft ya ce ya samar da wani tsari da zai taimaka wajen dakatar da harin, amma mutane da dama ba su fara amfani da shi ba tukuna.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu kasashen sun yi taron manema labarai don kamo bakin zaren

Sharhin Dave Lee, wakilin fasaha BBC a Arewacin Amurka

Akwai tambayoyi masu tsauri ga wadanda ba su dauki matakan kare na'urorinsu daga wannan harin ba, ciki har da ma'aikatun da hakkinsu ne su hana faruwar wannan harin tun da farko - watau hukumar tsaron Amurka, NSA da kamfanin na Microsoft.

Hukumar tsaron Amurka, NSA ta tanadi makamai na manhaja dabam-dabam domin kai hare-hare, amma kamfanin Microsoft ya sha sukar halayyar, inda ya kira shi abu mai hatsari.

Idan an gano wata kafar da zata iya cutar da al'umma, lallai sanar da Microsoft shi ne abu mafi kyau domin a toshe kafar, in ji Microsoft.

Amma akwai batun hakkin da ke kan Microsoft na samar da kariya ga abokan huldarsa - ba kamar yadda yake fifita masu biyansa wasu kudade na musamman ba.

Samar da kariya ga na'urar daya abu ne mai sauki, amma inda ake da dubban na'urori kamar hukumar NHS fa? Abu ne mai wahala, mai dan karen tsada kuma mai sarkakiya sosai.

Bayanan kamfanin Microsoft na kin samar da kariya ga na'urori irin na NHS har sai sun biya wasu kudade na musamman ya zama tamkar karban kudaden fansa shi ma.

Labarai masu alaka