'Yadda na yi shigar maza don na samu aiki'

Pili Hakkin mallakar hoto UN WOMEN
Image caption Pili Hussein mai yin shigar maza

Pili Hussein ta so ta yi arziki ta hanyar hako wani dutse mai daraja da aka ce ya fi daimon daraja sau dubu, amma tun da mata ba su da damar yin aikin hakar ma'adinai, sai ta yi shigar maza tana aiki da abokan aikinta na tsawon shekaru.

Pili Hussein ta taso a cikin wata babbar zuri'a a kasar Tanzaniya. Babanta yana kiwon tsuntsaye kuma yana da manyan gonaki masu yawa, yana da mata shida da 'ya'ya 38.

Ko da yake ta samu cikakkiyar kulawa ta bagarori da dama, amma idan ta tuno da kuruciyata ba ta jin dadi.

Ta ce, "Babana yana dauka ta kamar namiji, har ma ya bani tsuntsayen da yake kiwo don na rika kula da su, ba na son irin wannan rayuwar kwata-kwata."

Ta yi rayuwar aure cikin kunci, wanda hakan ya sa ta gudu daga wurin mijin nata da yake azabtar da ita tana da shekara 31.

Pili ta ce, "Ban yi karatu ba, saboda haka ba ni da zabin yin rayuwa mai kyau."

Ta ce, "Ba a barin mata su yi aikin hako ma'adinai, saboda haka sai na yi shigar maza majiya karfi. Na dauki babban wando na yanke shi ya koma gajere na saka na yi kamar namiji."

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Ma'aikatan hako ma'adinai na bakin aiki.

"Ana kira na da Uncle Hussein, ban fadawa kowa cewa hakikanin suna na Pili ba. Ko yau ka je sansanin kana nema na Uncle Hussein za ka ce."

"Ina iya shiga karkashin kasa inda ake hako ma'adinai na tsawon mita 600, inda wasu mazan ba sa iya yin haka. Ina da karfi sosai, kuma ina yi ne don na tabbatar da cewa na yi duk abin da ake tsammanin namiji ne zai iya yi.

Pili ta ce, ba wanda ya taba zaton ita mace ce.

Ta ce, ina yin abu tamkar Gwaggon-biri, ina iya yin fada, magana ta ba dadi, ina iya daukar katuwar wuka kamar 'yan farauta. Ba wanda ya gane ni mace ce saboda duk abin da nake yi ina yi kamar namiji."

Bayan kamar shekara daya, ta yi arziki. Da kudin da ta samu ne ta ginawa Babanta da Babarta da kuma abokiyar tagwaitakarta gida, ta sayawa kanta kayayyaki masu yawa, ta kuma dauki ma'aikatan da za su fara yi mata aikin hako ma'adinai.

Shigar burtun da ta yi ya yi tasiri, inda tsautsayi ne ya sa kawai aka ganota. Sakamakon wani rahoto da wata mata ta bayar cewa, wasu daga cikin ma'aikatan ma'adinan sun yi mata fyade, inda aka kama Pili a matsayin wacce ake zargi.

Pili ta ce, lokacin da 'yan sanda suka zo wurin mazan, suna tambayar wa ya yi fyade, sai aka ce ,"Wannan mutumin ne" daga nan ne aka dauke ni aka kai ni ofishin 'yan sanda.

Ba ta da wani zabi, dole ta tona wa kanta asiri.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarar 1967 ne aka fara gano dutse mai daraja na tanzanite

"Ina alfahari da abin da na yi, domin ya mayar da ni mai arziki, amma dai na sha wahala."

Ta bukaci 'yan sanda da su nemo macen da za ta caje ta, bayan da aka tabbatar da haka ne aka sake ta ba tare da dadewa ba. Amma duk da haka, abokan aikinta sun kasa yarda cewa za a iya yaudararsu na tsawon lokaci irin haka.

Ta ce, "Duk da haka sun kasa yarda da 'yan sandan ma a lokacin da aka ce ni mace ce. Ba su yarda ba har sai lokacin da na yi aure a shekarar 2001 na fara haihuwa."

Samun miji a lokacin da kowa ya daukeka a matsayin namiji yana da wahala, amma daga karshe Pili ta samu nasara.

Pili ta samu nasara, inda a yau ta mallaki kamfanin hako ma'adinai da ma'aikata 70. Uku daga cikin ma'aikatanta mata ne, sai dai suna aiki ne a matsayin masu dafa abinci.

Ta ce, duk da cewa akwai mata da yawa da suke aiki a kamfanin ma'adinai fiye da lokacin da ta fara, sai dai har yau kadan ne ba su da yawa sosai.

Hakkin mallakar hoto AFP

Ta ce, "Wasu matan suna wanke duwatsu, wasu suna fasawa, wasu kuma suna dafa abinci. Amma ba sa yin aikin hakowar, zai yi wahala a samu matan da za su yi abin da na yi."

Nasarar da Pili ta samu ya ba da ta damar daukar nauyin karatun 'ya'yan 'yan uwanta sama da 30. Amma duk da haka ba ta son 'yarta ta gaji sana'arta.

Ta ce, "Ina alfahari da abin da na yi, don kwalliya ta biya kudin sabulu, amma fa na sha wahala."

Ta ce, "Ina so na tabbatar cewa 'yata ta yi karatu, ta yi ilimi don ta taimakawa rayuwarta ta wata hanyar daban, ba irin aikin da na yi ba."

Labarai masu alaka