Ɗaliban makarantar Firamare sun yi zanga-zanga a Kenya

Sai dai zanga-zangar ta kare cikin lumana. Hakkin mallakar hoto MOSES MUOKI/CAPITAL FM
Image caption Sai dai zanga-zangar ta kare cikin lumana

Ɗaliban makarantar Firamare, sun yi amfani da kujerun zamansu wajen rufe babbar hanyar birinin kasar Kenya wato Nairobi, bayan da aka rushe makarantarsu.

An rushe makarantar Kenyatta Golf Course Academy a karshen makon da ya gabata sakamakon rikicin da ake yi a kan filin.

Ɗaliban sun haɗu da iyayensu da Malamansu suna faɗar, "Muna son makarantarmu, muna son yin karatu a cikinta".

An rushe makarantun Kenya da dama a shekarun baya-bayan nan, saboda sa'insar da ake samu a kan shaidar mallaka.

Wani mai zanga-zanga daga cikin iyayen yara ya ce, "Muna yin zanga-zangar ne saboda ba a bamu wata sanarwa ta barin makarantar ba".

Malaman makarantar sun bayar da rahoton cewa, rushe makarantar na damunsu, saboda hakan na iya jawo musu asarar rasa aikinsu.

Sai dai zanga-zangar ta kare cikin lumana.

Shekara biyu da ta gabata, 'yan sanda sun watsa wa 'yan makaranta hayaki mai sa hawaye a Nairobi bayan da aka sayar musu da filin da suke wasa.

Labarai masu alaka