Fyade: Mata suna rayuwa cikin fargaba a India

Indiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu gwagwarmaya na cewa har yanzu mata na fuskantar barazana a kasar

'Yan sanda a jahar Haryana da ke arewacin Indiya na binciken wani gagarumin fyade wanda ya firgita mutanen Kasar.

Da farko dai 'yan sandan sun ce an tsinci gawar wata mata 'yar shekara 23, da suka ce ta mutu ne bayan da aka yi mata fyade a makon da ya gabata, a gundumar Rohtak.

An dai dauki kwanaki kafin a gano gawarta wacce ta fara lalacewa. Binciken da aka yi wa gawar na nuna cewa "kokon kanta ya fashe".

'Yan sandan sun ce ranar Asabar ma an yi wa wata yarinya 'yar shekara 22 fyade, a cikin wata mota da ke tafiya a yankin Gurgaon da ke birnin Delhi.

Masu gwagwarmaya dai na cewa wannan lamari na kara nuna cewa har yanzu mata na ci gaba da fuskantar barazanar rashin tsaro a kasar.

Mazauna gundumar Sonipat, inda iyalan wacce aka yi wa fyade a Rohtak ke zaune, su ne suka tsinci gawar matar bayan da karnuka suka fara cinyeta.

Babban jami'in 'yan sanda na yankin Ashwin Shenvi ya shaida wa BBC cewa, "Mun kama mutane biyu kwana daya bayan faruwar lamarin kuma sun amsa laifin".

"Binciken gawar ya nuna cewa ta rasu ne sakamakon raunukan da ta ji bayan an yi mata fyade".

An yi wa 'yan matan gidan marayu fyade a Indiya

An yi ma wata mata fyade cikin bus a Indiya

Binciken ya nuna an ba ta kwayoyi ne kafin a yi mata fyaden. Ana dai zargin cewa daya daga cikin mutanen ya santa.

Kwamishinan 'yan sanda na gundumar Gurgaon, Sumit Kumar ya ce an yi garkuwa da budurwar kuma ana zargin an yi mata fyaden ne a cikin motar da ke tafiya ranar Asabar da daddare.

Ya ce "har yanzu ba mu kama kowa ba, amma muna bin hanyoyi da dama, wadanda ba za mu bayyanawa manema labarai su ba,".

Fyade da cin zarafin mata dai a kasar ta Indiya, na ci gaba da yaduwa tun shekarar 2012, lokacin da aka kashe wata daliba bayan an yi mata fyade a cikin wata motar bas a birnin Delhi.

Haka kuma, lamarin fyade ga mata da kananan yara na ci gaba da ruruwa kamar wutar daji a ko'ina cikin kasar.

Labarai masu alaka