Za a zubar da cikin 'yar shekara 10 a India

Yaran makaranta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dokar Indiya bata yarda a zubar da ciki ba idan har ya yi wata biyar

Kungiyar wasu likitotci na ganawa a Indiya domin yanke hukunci kan ko za a iya zubar da cikin wata yarinya mai shekara 10 da aka yi wa fyade.

'Yan sandan garin Rohtak da ke arewacin kasar sun shaida wa BBC cewa mijin mahaifiyar yarinyar ya sha yi mata fyade kuma nan da wata hudu za ta haihu.

An kama mijin mahaifiyar kuma yana hannun 'yan sanda har sai lokacin da aka kammala cikakken bincike.

Dokar Indiya ba ta yarda a zubar da ciki ba idan har ya yi wata biyar, sai dai idan har likitotci sun gamsu cewa rayuwar matar da ke dauke da cikin na cikin hadari.

An gabatar da dokar mai tsanani ne domin yaki da banbancin da ke tsakanin jinsi.

Dadaddiyar al'ada ta nuna son yara maza fiye da 'ya'ya mata ya jawo mata sun zubar da miliyoyin cikin 'ya'ya mata bayan gwaji ya tabbatar musu cewa suna dauke da cikin 'ya mace.

A watannin baya-bayan nan kotun kolin Indiya ta samu kararraki, wasu na mata da aka yi wa fyade wadanda suke so zu zubar da cikin bayan wata biyar.

Duk sanda aka kai wa kotun irin kararrakin, ta kan mikawa kwararru a harkar lafiya.

A lamarin baya-bayan nan da ya faru a garin Rohtak da ke jihar Haryana, likitoci daga cibiyar kimiyar lafiya na ganawa domin yanke shawara a kan bukatar iyayen yarinyar na a zubar mata da cikin da take dauke da shi.

A makon da ya gabata ne aka gano cewa yarinyar na dauke da juna biyu, a lokacin da mahaifiyarta 'yar shekara 10 wacce ke aikin shara da wanke-wanke a wani gida ta kai 'yar asibiti bayan ta yi zargin cewa 'yar tana da juna biyu.

Rahotanni sun ce mahaifiyar yarinyar na barinta a gida a lokutan da take zuwa wurin da take yin aiki. Ta shaidawa mahaifiyarta cewa mijinta yana yi mata fyade kuma ya gargade ta kar ta gaya wa kowa.

Pankaj Nain, babban jami'in 'yan sandan Rohtak ya shaidawa BBC cewa an kama mutumin bayan an kai kararsa wurin 'yan sanda.

Labarai masu alaka