Almundahana: Riga-kafi ya fi magani — Saraki

Saraki Hakkin mallakar hoto Twitter Saraki
Image caption Sanata Saraki ya yi wannan jawabi a wajen taron kaddamar da littafi kan cin hanci

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya yi kira da cewa kamata ya yi a fi mayar da hankali wajen hana almundahana maimakon yin horo, idan ana so a yi nasara ta din-din-din a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa a kasar.

Sanata Saraki ya yi wannan magana ne a yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da wani littafi da Sanata Dino Melaye ya rubuta a kan cin-hanci da rashawa a Najeriya, mai taken Antidotes For Corruption - The Nigerian Story.

Da yake magana a kan dalilin da ya sa yake ganin daukar matakan riga-kafi sun fi, Sanata Saraki ya ce, "Na gamsu cewa dole mu koma kan wannan maganar da muka saba ji cewa riga-kafi ya fi magani.

"Ta yiwu dalilin da ya sa ba a yi nasara a yaki da cin hanci da rashawa ba shi ne, watakila mun fi daukaka horar da mutum fiye da daukar matakin hana faruwar hakan.

"Wajibi ne mu sake nazari a kan hanyoyin da muke bi ta yadda za mu samar da wani tsari wanda zai sa aikata almundahana, ko samar wa kudin da aka samu ta hanyar almundahana maboya a cikin kasarmu, ya yi wahala.

"Yayin da muke kokarin cimma hakan, lalle ne mu dauki matakan tabbatar da gaskiya, sannan mu rage ikon da jami'ai ke da shi na aikata abin da suka ga ya dace yayin kashe kudin al'umma, sannan mu karfafa tsarin yin komai a bayyane".

Akwai rashin jituwa tsakanin Buhari da Saraki?

Nigeria: Majalisa ta juya wa Buhari baya kan nadin Magu

Bayan haka kuma shugaban na Majalisar Dattawan Najeriya ya kara da cewa, su a majalisa a makon da ya gabata sun dauki babban matakin fara aiwatar da komai a bayyane.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Shugabannin majalisar dokokin Najeriyar rike da littafin da aka kadamar

Da yake magana a kan dokar yaki da cin-hanci da rashawa, ya ce a yanzu haka majalisar na kokarin ganin an gabatar da kudurorin doka daban-daban, kamar kudurin dokar ba da kariya ga masu tona asirin barayin dukiyar gwamnati wadda za a gabatar da ita nan da watan Yu

Akwai kuma kudurin doka a kan yadda ya kamata a yi da kudaden da aka kwace wadanda aka same su ta hanyar da ba ta halalta ba da kuma kuma kudurin dokar samar da kotu ta musamman ta yaki da cin-hanci da rashawa.

Wasu 'yan Najeriya dai ka iya fassara wadannan kalamai na Mista Saraki da jurwaye mai kamar wanka; musamman ganin cewa shi kanshi yana fuskantar tuhume-tuhume da suka danganci amfani da matsayinsa don biyan bukatunsa na kashin-kai.

A baya-bayan nan dai an yi ta samun takun-saka a tsakanin bangaren zartarwa da bangaren majalisa a kan batutuwa daban-daban, ciki har da kin tabbatar da shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu.

Wannan al'amari ya janyo ce-ceku-ce a kasar, inda wasu da dama ke ganin bangaren majalisar na yin zagon-kasa ga yaki da cin hancin da shugaba Buhari ke yi.li.