Harsunan Najeriya na fuskantar barazanar bacewa

Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Wadanda suka halarci taron raya harsunan Najeriya a Kaduna, Najeriya

Ministan watsa labarai da ala'adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya nuna takaicinsa da yadda harsunan kasar da dama ke fuskantar barazanar bacewa.

Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Kaduna na arewa maso yammacin kasar lokacin bude wani taron kwana biyu a kan tasirin jaridun da ake wallafa su da harsunan kasar.

Cibiyar Raya Al'adu ta Kasa (NICO) tare da Ma'aikatar Watsa Labarai da Al'adu ne suka shirya taron mai taken "Alakar Jaridun Harsunan Kasa da Gina Kasa".

Ministan ya ce akwai "gagarumin koma-baya wajen amfani da harsunan kasar mu", sannan ya koka da yadda "yawancin mutanen kasar ba sa iya rubutu ko karatu da harsunan su na gado".

Ya lura cewa jaridun da ake wallafawa cikin harsunan kasar na ainihi suna taka muhimmiyar rawa wajen farfado da harsunan da ke fuskantar barazanar shudewa.

Ministan ya ce tuni ya ziyarci irin wadannan jaridun kamar Alaroye, daIroyin Owuro, da Rariya, da Aminiya,da Leadership Hausa, domin gano hanyoyin da za a bi don raya su a wannan lokacin da jaridu ke fuskantar "gagarumin kalubale".

Gwamnatin ta Najeriya ta bayyana shirinta na fassara wasu littattafan kasar kamar The Lion and the Jewel da The Passport of Mallam Ilia da kuma Things Fall Apart zuwa harsuna daban-daban.

Tana fatan ta wallafa su zuwa littafai masu zane watau comics da shirye-shiryen talabijin da fina-finai domin a ci gajiyar tsarin kafofin watsa labarai na zamani, watau digital media, domin taimaka wa harsunan.

Gwamnatin tana kuma son kawar da tasirin kafofin sadarwa na zamani, wato social media,da YouTube wajen samar wa al'umomin kasar hanyoyin zamani da za su koyi wadannan harsunan masu bacewa.

An samar da shafuffukan intanet domin samar wa mutane wuraren wasa kaifin sanin harsunan kasar.

Ministan ya kalubalanci kowa da ya "dage wajen samar da hanyoyi da shawarwari a kan irin matakan da ya kamata gwamnati ta dauka domin cimma burinta".

Shugaban kamfanin jaridun Leadership, Mista Sam Nda-Isaiah, wanda shi ne ya gabatar da babban jawabi a wajen taron, ya kira jaridun da ake wallafawa cikin harsunan kasar a matsayin "mabudin samar da ci-gaban kasa".

Amma ya ja hankalin masu wallafa jaridu da su tafiyar da su "tamkar sauran jaridu, wato kamar kamfanonin kasuwanci masu neman riba".

Babban sakataren Cibiyar Raya Al'adu ta Kasa, watau NICO, Mista Barclays Ayakoroma, ya bayyana harsunan kasar da cewa "wani sinadarin da zai farfado da al'adun kasar, kuma mai iya hada kan jama'ar kasar baki daya".

Labarai masu alaka