Satar mutane don neman fansa a Nigeria na ƙaruwa

Nijeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokuta da dama wadanda aka yi garkuwa da su kan rasa rayukansu idan aka taki rashin sa'a

Wani basarake Gorionla Oseini a birnin Legas da ke kudu maso yamma a Nijeriya ya tsammaci samun baƙi da yammacin wata rana a fadarsa amma bai taɓa tunanin cewa masu satar mutane ba.

''Ina shirin kwanciya a lokacin, sanye da gajeren wando, (sai ga su) sun yi ta harbin kan mai tsautsayi, har suka harbi ɗaya daga cikin fadawana, da kuma wata matata.''

Daga nan sai aka kai basarake Gorionla cikin wani surƙuƙi cike da tsirrai da koramu a wajen birnin Legas, inda wani kwale-kwale ke jira.

Satar mutane don neman kuɗin fansa na daɗa ƙamari a Najeriya, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziƙi mafi tsanani a shekaru gommai.

A katafaren birnin Legas kadai, an ba da rahoton sace fiye da mutum 50 a baya-bayan nan.

Ko da yake, masu fashin baƙi kan sha'anin tsaro sun ce gaskiyar lamarin ta fi adadin da aka bayar, don kuwa ba a cika kai rahoton yawancin sace-sacen mutanen da ake aikatawa ba.

'Yan uwan wadanda aka sace sun fi son biyan fansa maimakon sanar da 'yan sanda.

Wasu wadanda aka yi garkuwa da su a lokuta daban-daban a birnin Lagos sun shaidawa BBC irin halin da suka shiga da cewa abin firgici ne.

''Na ga masu garkuwa da mutane fiye da ashirin da idanuna.''

'' Sun yi ta harbe-harbe, na gudu sai suka bini da gudu suna cewa tsaya, tsaya! Suna cewa za su harbe ni, amma ban tsaya ba, na dauka ina mafarki ne.''

An yi garkuwa da wani mai sarautar gargajiya, da wani mai kula da gona da kuma wani mai aikin karfi na tsawon mako guda ko fiye da haka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Garkuwa da mutanen domin neman kudin fansa ya kara ta'azzara a Nijeriya

A da wadannan mutanen da suke yin garkuwa da su, suna satar danyen mai ne daga bututan da suka bi ta cikin koramu, amma a yanzu suna satar mutane ne domin neman kudin fansa.

Mai kula da gona Adelike Adejare ya siffanta wahalar da ya jure ta tsawon makonni;

''Abin da suka fara yi da muka je can sun lakada mana duka, an dake mu saboda azaba mun dauka karashen rayuwarmu kenan.''

Cimma matsaya kan kudin fansa ba abu ne mai sauki ba, kamar yadda sarki Gorionla ya shaidawa BBC;

''Mutanena sun biya kudin fansa, amma bayan an biya kudin, manyan sai suka raba kudin tsakaninsu su gudu, sai bayan haka kananan suka yi shelar cewa za a fara wata sabuwar yarjejeniya.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba kowa ne ke iya biyan kudin fansa ba ga masu garkuwa da mutanen

Amma kuma ba kowa yake da karfin biyan kudin fansa ba.

An sace Abbey Sino Gilbert a lokacin yana aiki a wani gidan kaji;

''Sun nemi a biya dala 1,500 a kan ko wane mutum, sai maigidana ya ce shi dala 500 zai iya biya, amma sai suka ki, daga nan tattaunawar ta watse.''

Daga bisani dai Abbey ya zama 'yantacce, kuma an saki sauran mutanen biyu bayan da aka biya kudin fansar.

Matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansar dai ta zama babbar barazana a tsakanin al'ummar Najeriyar, ganin yadda a wasu lokutan a kan taki rashin sa'a sai ka ga wadanda aka yi garkuwar da su sun rasa rayukansu garin kokarin ceto su, ko kuma idan aka dau tsawon lokaci ba a kai wa masu garkuwar kudin fansar ba.

Labarai masu alaka