'Yan mata a Indiya na yajin cin abinci saboda cin zarafi

Indiya
Image caption Dalibai na zangan-zanga tsawon kwanaki shida

Kimanin kwana shida kenan dalibai mata 13 ke yajin cin abinci a Indiya, domin nuna rashin amincewarsu da cin zarafin da suke fuskanta a jihar Haryana ta arewacin Indiya.

'Yan matan wadanda shekarunsu ke tsakanin 16 da 18 sun shaidawa BBC cewa, maza na yawan yi musu maganganun batsa idan suna kan hanyarsu ta zuwa makaranta daga kauyukansu.

'Yan matan sun kara da cewa 'yan sanda a gundumar Rewari sun ki daukar wani mataki na kare su.

A yanzu 'yan sanda sun yi alkawarin za su inganta harkokin tsaro da kare 'yan matan.

Gwamnati ta kuma yi alkawarin za ta gina makarantar sakandare a kauyen domin 'yan matan su daina yi zirga-zigar zuwa wasu kauyukan don halartar makaranta.

A halin yanzu, daliban wadanda ruwa kawai suke sha amma ba sa cin abinci, sun ce ba za su daina yajin cin abinci ba sai dai gwamnati ta ba su rubutaccen tabbaci.

Wasu iyaye da daliban ba sa yajin cin abincin, amma suna goyon bayan zanga-zangar.

Image caption Sheetal, a hannun dama ta ce ba zata daina yajin cin abinci ba sai gwamnati ta aminci da bukatarsu

Daya daga cikin dalibai 13 Sheetal ta ce, "Ko wacce rana muna fuskantar cin zarafi.''

"Wannan yana nufi, mu daina karatu ko mu daina fatan samur kyakkyawar rayuwa? Masu arziki da 'ya'yansu kawai ya kamata su yi fatan samun kyakkyawar rayuwa? Gwamnati ta kare mu ko kuma ta bude mana makarantar sakandare a kauyenmu.''

Sujata kuma ta ce, ''Mazan na kokarin taba mu yadda bai dace ba.''

''Sun rubuta lambobin wayoyinmu a kan bango kuma suna mana kalaman batsa. Gaskiya abin da yafi hakan ma na faruwa amma ba komai zamu iya bayyanawa ba.''

Nitin Srivastava daga BBC Hindi, Rewari

'Yan matan na cikin tsaka mai wuya a wannan mako da suke neman a inganta harkokin ilimi da tsaro a kauyensu. Iyayensu kuwa na goyon bayansu ta hanyar ajiye kayan aikin.

Haryana na daya daga cikin jihohi a Indiya da maza suka fi mata yawa kuma an saba cin zarafin mata.

Amma wannan ne karon farko da yaran matan suka yi zanga-zanga a kan lamarin. Sun samu goyon bayan al'ummar yankin, har da maza da ke da ra'ayin cewa kamata ya yi a daraja mata.

Daya daga cikin mahaifan daliban ta ce, ''Muna cikin bacin rai idan wadannan 'yan mata na wahala.''

Ta kara da cewa, ''Wadannan 'yan mata na fuskantar irin cin zarafi da ba zan iya bayyanawa ba. Idan muka kai kara wajen 'yan sanda sai su matsa mana mu koma da irin wadannan kararraki.''

Image caption Sujata,a hannun hagu ta ce ina son in ci gaba da karatu

Mahaifin daya daga cikin yaran da ke zanga-zangar, Rohtash Kumar ya ce matsalar cin zarafin mata, abu ne dake faruwa shekaru da dama.

Ya kara da cewa, ''Wannan ne karon farko da 'yan matan suka dau mataki kuma mazan kauyen na goyon bayansu.''

Mista Kumar ya ce yana son ya ga tabbaci cewa za a aiwatar da sauye-sauyen da 'yan sanda da jami'ai suka yi alkawari.

''A baya ba su cika alkawarinsu ba. Muna son mu tabbatar cewa gwagwarmayarmu ba ta tafi a banza ba,'' in ji Mista Kumar.

Labarai masu alaka