Tsibiri mafi yawan dattin roba a duniya

Henderson Island is part of the UK's Pitcairn Islands group Hakkin mallakar hoto The University Of Tasmania
Image caption Tsibirin Henderson wani bangare ne na rukunin tsibiran Pitcairn da ke Birtaniya

Wani tsibiri mai nisa da ke yankin kudancin tekun Pacific maras mutane shi ne yafi kowane wuri dattin robobi a duniya, in ji wani bincike.

Tsibirin Henderson, wanda yake cikin jerin tsibiran Pitcairn, yana da tarin bolar da ta kai miliyan 37.7 a gabar tekunsa.

Tsibirin yana tsakiyar wata igiyar teku, wadda ke debo bola daga jiragen ruwa masu wucewa, har ma daga nahiyar kudancin Amurka.

Masu bincike suna fatan wannan lamarin zai jawo hankalin jama'a ga illar amfani da robobi.

Binciken na hadin gwiwa ne tsakanin kasashen Austreliya da Birtaniya wanda ya tabbatar da yawan bolar ya kai robobi 671 a kowane murabbu'in mita daya, wanda jimillarsa ta kai ton 17.

"Yawancin bolar da ke tsibirin na Henderson kaya ne da muke amfani da su sau daya mu jefar," in ji Dr Jennifer Lavers ta Jami'ar Tasmania.

An wallafa wannan binciken ne a wata mujallar kimiyya mai sunan "Proceedings of the National Academy of Sciences", inda ta bayyana tsibirai masu nisa sun zama tamkar wani "kwatami" ga bolar duniya.

Hakkin mallakar hoto The University Of Tasmania

Banda kayan masunta, tsibirin na Henderson ya tara bolar kayayyakin rayuwar yau da kullum, kamar buroshin goge hakora da laitar kunna taba da rezoji.

"Akwai halittu kamar kaguwar tudu da suka mayar da murafan kwalba da robobi a matsayin gida," Dr Lavers ya fada wa BBC.

"Da farko za ka dauka abin yana da ban sha'awa, amma batun ba na sha'awa ba ne. Robobin sun tsufa, ga su da tsini da kaifi, kuma suna da sinadari mai cutarwa.

An gano hulunan robobi "iri daban-daban, kala daban-daban, manya da kanana," in ji malamar kimiyyar.

Tasirin bolar

Hukumar UNESCO ta zayyana tsibirin na Henderson a matsayin wani kebabben wuri mai halittu na musamman masu bukatar kariya. Akwai tsirrai guda 10 da nau'in tsuntsaye iri hudu da suke rayuwa a tsibirin.

Tsibirin na da nisan kilomita 190 (mil 120) daga tsibirin Pitcairn, mai nisan kilomita dubu biyar daga kasar Chile, a tsakiyar wani wani makeken kugiyar teku mai suna "South Pacific Gyre".

Dr Lavers ta ce halin da wannan tsibirin ke ciki yana haska tasirin da bolar robobin ke da shi a kan yanayin duniya.

Hakkin mallakar hoto The University Of Tasmania
Image caption Masu bincike sun kiyasta cewa bolar da take wajen ta kai tarin abubuwa miliyan 37.7

"Kusan dukkan tsibirai da jinsunan duniya suna fama da wannan matsala ta yawan bolar da dan Adam yake samarwa.

"Babu wani mutum ko wata kasa a duniya da bata da alhakin wannan halayyar."

Ta ce bolar robobi na raunata halittun cikin teku baki daya.

Cibiyar Binciken Teku ta Jami'ar Tasmania da Cibiyar Tattalin Kimiyya tare da Kungiyar Kare Tsuntsaye na Ingila suka hada wannan binciken.

Greg Dunlop na BBC ne ya hada wannan rahoton.