Shakar man fetur tsakanin matasa na ƙaruwa a Australia

Wani yaro dake kokarin zukar mai daga wani jirgin sama Hakkin mallakar hoto ABC
Image caption An kai yara tara yankin Darwin da ke arewacin kasar domin a basu kulawa

Wani bidiyon tsaro ya nuna yadda wasu yara ke shiga filin jirgin saman tsibirin Elcho kuma suke zuke mai daga cikin jiragen saman.

Shakar fetur ba wani sabon kalubale bane a al'ummomi, amma man jiragen sama sunfi hadari saboda suna dauke da dalma a cewar jami'an.

Dalma na iya lalata kwakwalwa da hanyoyin jijiyoyi da ke jikin dan adam.

Jami'an lafiya sun yi amannar cewa daga cikin ko waddane matasa sama da 100 a kan samu yaro mai shekara bakwai na shakar mai a tsibirin Elcho da kuma wani yanki da ke kusa da wurin a watan Maris din shekarar da ta gabata.

John Gurrumgurrum Burarrwanga ya shaidawa kafar yada labarai ta Austrelia cewa, "Yaranmu na karewa a asibiti sakamakon sinadiran da suke shaka wanda bashi da kyau ga lafiyarsu."

An kai yara tara yankin Darwin da ke arewacin kasar domin a basu kulawa.

Image caption Hukumomi za su zage damtse domin samun mafita

Shugaban Miwatj, John Morgan ya ce lamarin abin tayar da hanakali ne kuma abin damuwa ne".

"Tawagarmu da ke yankin a matsayin wani bangare na al'ummar na aiki ba dare ba rana domin taimaka wa iyalai domin su kare aukuwar irin wadannan lamuran," kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya aikewa BBC.

Mai magana da yawun gwamnan yankin arewa, Jim Rogers ya ce hukumomi za su zage damtse domin samun mafita.

Gwamnati ta riga ta ware dala 52,000, ta yadda ma'aikatan tsaro za su dinga yin gadi tare da sintiri a filin jirgin saman tsibirin Elcho da daddare a cewar sa.

Mista Rogers ya ce "Muna aiki tare da Miwatj da ma'aikatan lafiya da kuma shugabannin al'ummomi domin gano dalilin da yasa ake samun aukuwar lamarin kuma mu tabbatar cewa mun mayar da hankulanmu inda ya kamata."

Hakkin mallakar hoto ABC
Image caption Hukumar lafiya ta duniya ta ce dalma zai iya jawo rashin lafiyar da ba za a iya warkewa

Hukumar lafiya ta duniya ta ce, dalma za ta iya jawo rashin lafiyar da ba za a iya warkewa ba, musamman ga yara kanana.

Labarai masu alaka