Tattalin arzikin Nigeria na farfadowa—Adeosun

Mrs Kemi Adeosun ta ce gwamnati na bada tallafin kudi ga jama'a masu karamin karfi Hakkin mallakar hoto TWITTER/KEMI ADEOSUN
Image caption Mrs Kemi Adeosun ta ce gwamnati na bada tallafin kudi ga jama'a masu karamin karfi

Ministar kudin Najeriya, ta ce sannu a hankali kasar na fita daga halin karayar tattalin arziki mafi muni da ta shiga.

A wata hira da BBC, Mrs Kemi Adeosun ta ce suna da kwarin gwiwar cewa farfadowar mai dorewa ce.

Ministar ta bayyana takacin ta kan yadda irin wahalar da talakawa ke fuskanta sakamakon mawuyacin halin da tattalin arziki ya shiga inda ta ce matakan da gwamnati ta bullo da su na tasiri wajen rage tsadar rayuwa ga talaka.

Mrs Adeosun ta ce " ba talakawa ne kadai a Najeriya ke fama da matsala na halin rayuwa na matsin da kasar ta shiga sakamakon raguwar kudaden shigar da gwamnati ke samu da kusan kashi 50 cikin 100, amma abin da zan ce shi ne muna fitowa da manufofi da ke ragewa mutane wannan radadin" in ji Adeosun.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce ta fara bada tallafin kudi ga jama'a masu karamin karfi tare da ciyarda dalibai a makarantu wadanda aka tsara da nufin tallalafa wa talakawa.

Haka kuma gwamnati ta bullo da shirin N Power dake samarwa matasa da suka kammala karatu ayyukan yi.