Nigeria: Ce-ce-kuce ya kaure a PDP kan zabukan kananan hukumomin Legas

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Nan gaba ne dai kotun kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan sahihin shugaban PDP tsakanin Makarfi da Sheriff

A Najeriya ce-ce-kuce ta kaure a tsakanin bangarori biyu na babbar jam'iyyar adawa ta PDP game da zabukan kananan hukumomin da za a gudanar a jihar Legas.

Bangaren Sanata Ahmed Muhammad Makarfi na zargin bangaren Sanata Ali Modu Sheriff da yunkurin hana PDP cin zabe.

Mai magana daga bangaren Makarfi, Abdullahi Jalo, ya ce a jihar Delta 'yan bangarensu sun shiga jam'iyyar Accord Party domin kaucewa yunkurin hana PDP cin zaben da bangaren Ali Modu Shariff ya yi a zabukan da aka gudanar a jihar ta Delta.

Bangare Ali Modu Sheriff ya musanta hakan, yana mai cewa bangaren Sanata Ahmed Muhammad Makarfi ne ke neman kawo cikas a zabukan kananan hukumomin da ke gaban jam'iyyar a jihar Legas.

Bangaren na Sheriff ya kara da cewar kotun daukaka kara ta riga ta tabbatar da Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban jam'iyyar PDP.

Mai magana daga bangaren Ali Modu Sheriff, Bashir Medugu, ya ce wadanda suka nemi 'yan takaran jam'iyyar PDP su je su tsaya a wata jam'iyya ne ke neman dagula wa jam'iyyar lissafi.

Amman wani jigo a jam'iyyar PDP a Legas, Alhaji Armaya'u Umar, ya ce dukkan bangarorin biyu 'yan jam'iyyar PDP ne kuma za su yi iya kokarinsu domin cimma nasara a zabukan kananan hukumomin da ke tafe a jihar.

Labarai masu alaka