Nigeria: Buratai ya gargaɗi sojoji kan shiga harkokin siyasa

Laftanar Kanal Tukur Buratai ya ce ya samu bayanai ne da ke nuna cewa wasu mutane suna tunkarar wasu jami'an soji kan wasu dalilai na siyasa Hakkin mallakar hoto Nigerian Army Twitter
Image caption Laftanar Kanal Tukur Buratai ya ce ya samu bayanai ne da ke nuna cewa wasu mutane suna tunkarar wasu jami'an soji kan wasu dalilai na siyasa

Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Laftanar Kanal Tukur Buratai ya gargaɗi sojojin kasar da su guji yin mu'amala da 'yan siyasa ko shiga cikin al'amuran siyasar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar, babban hafsan sojin ya ce ya samu bayanai ne da ke nuna cewa wasu mutane suna tunkarar wasu jami'an soji kan wasu dalilai na siyasa da ba a bayyana ba.

Sanarwar ta ce a don haka ne Laftanar Kanal Buratai ya gargaɗi sojojin da su guji irin wannan halayya.

Laftanar Kanal Buratai ya kuma tunatar da su cewa akwai ƙwarewa a rundunar sojin Najeriya da ɗa'a da amana da kuma kasancewar ta wata hukuma mai bayyanannen kundin tsarin mulki da irin nauye-nauyen da ke kanta.

Buratai ya umurci sojoji su bayyana kadarorinsu

Burutai ya mallaki kadarori a Dubai

An yi yunkurin hallaka Burutai — Sojoji

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army Twitter
Image caption Laftanar Kanal Tukur Buratai ya ce akwai amana da da'a a aikin soja

Sanarwar ta kara da cewa, Laftanar Kanal Buratai ya yi gargadi mai tsanani ga jami'ai da sojojin da suke da sha'awar siyasa cewa gara su yi murabus.

"Duk wani jami'i ko sojan rundunar sojin kasa da aka samu da irin wannan halayya ta shiga cikin al'amuran siyasa ko al'amuran da ba sa cikin aikin soja, to duk abin da ya same shi sai ya zargi kansa da kansa," in ji Laftanar Kanal Buratai a cikin sanarwar.

Babban hafsan rundunar sojin kasar ya nanata cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da nesanta kanta da al'amuran siyasa za kuma ta ci gaba da girmama dokar kasa.

Labarai masu alaka