Uganda ta dakatar da nuna fim din luwadi

An fitar da fim din tun shekara ta 2010 kuma ana shirin nuna shi a wani bikin nuna fina-finan Turai a Uganda. Hakkin mallakar hoto INFINITY FILM & TV
Image caption An fitar da fim din tun shekara ta 2010 kuma ana shirin nuna shi a wani bikin nuna fina-finan Turai a Uganda.

Hukumar tace fina-finai ta kasar Uganda ta hana nuna wani fim din kasar Holland mai suna The Dinner Club, bayan da hukumar ta ce fim din yana "daukaka luwadi", in ji ofishin jakadancin kasar Holland da ke Kampala.

Luwadi dai babban laifi ne a Uganda.

Ofishin jakadancin ya bayyana "takaici" game da hana nuna fim din.

Daga baya ofishin jakadancin ya wallafa jerin dalilan da hukumar tace fina-finan ta bayar, wadanda suka hada da "amfani da kalaman banza" da "nuna mata suna shan taba".

Hukumar tace fina-finan ta ce nuna matan da suka hada wani "kulob din cin abincin dare, a zahiri gidan karuwai ne kawai", kuma fim din yana nuna wasu "'yan luwadi sun yi tatil da giya".

Ta ce "akwai wurin da ake kambama luwadi, har wasu mata suke sukar aure, har suna cewa auren maza wahala ne! Wannan ya ci karo da al'adun Uganda."

Hukumar kuma ta soki wani wurin da wani namiji ya kira wani namijin "yarinyar da ta hadu".

Ce-ce-ku-ce aUganda

Mutane da dama sun goyi bayan matakin da hukumar ta dauka, a shafin da aka wallafa labarin na Facebook.

Wani ya rubuta cewa, "Ya kamata mutanen kasashen yammacin Turai su sani cewa kasar Uganda tana da al'adu, kuma babu laifi idan aka dakatar da dukkan abin da ake ganin mugun abu ne, ko wanda zai iya lalata mana al'adu".

Amma ofishin jakadancin Holland a Uganda ya sami goyon baya daga wasu mutanen kasar, har wani yana rubuta, "Wannan abin takaici ne. Wanda ya wallafa wannan rahoton ba ya wakiltar mafi yawan jama'ar kasar Uganda. A gaskiya wannan ya kunyata 'yan Uganda masu yawa".

An fitar da fim din tun shekara ta 2010 kuma ana shirin nuna shi a wani bikin nuna fina-finan Turai a Uganda.

A yanzu haka ofishin jakadancin kasar Holland ya sanar da janyewar kasar daga wannan bikin nuna fina-finan sakamakon matakin da kasar Ugandan ta dauka.

Labarai masu alaka