Indonesia: Za a yi wa 'yan luwadi bulala 85 a bainar jama'a

A lokacin da aka yankewa mazan hukunci sun rufe fuskokinsu da rigunansu da kuma hannayensu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A lokacin da aka yankewa mazan hukunci sun rufe fuskokinsu da rigunansu da kuma hannayensu

Wata kotun shari'ar Musulunci ta lardin Aceh, a kasar Indonesiya, ta yankewa wasu maza biyu hukuncin bulala 85 a bainar jama'a a kan kama su da laifin yin luwadi.

An kama mutanen ne da laifin karya dokar shari'ar Musulunci wadda ake girmamawa a lardin Aceh, inda za a yi wa ko wannen su bulala 85.

'Yan sintiri ne suka kama mutanen a kan gado tare, a wannan watan na Mayu. Daya dann shekara 20 ne dayan kuma dan shekara 23, sai dai ba a bayyana sunayensu ba.

A lardin Aceh ne kawai aka fi tabbatar da aiki da dokokin shari'ar Musulunci a kasar.

Za a yi musu hukuncin ne a mako mai zuwa.

A baya ana yi wa mutane bulala a bainar jama'a ne kawai a bisa kama su da laifin shan giya da caca.

A shekarun baya-bayan nan ne, lardin Aceh ya kara kaimi wajen ra'ayin mazan jiya. A shekarar 2014 ne aka gabatar da tsauraran dokoki a kan masu aikata luwadi, kuma dokar ta fara aiki a shekarar da ta biyo baya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutanen na kulle tun daga lokacin da aka kama su

A cewar kamfanin dillanci labarai na AFP, Alkali Khairil Jamal ya shaida wa kotu cewa, "Mutanen sun tabbatar da cewa sun aikata laifin luwadi".

A lokacin da aka yanke wa mutanen hukunci, sun rufe fuskokinsu da hannayensu.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na masu fafutuka sun yi Allah-wadai da hukuncin da suka kira 'tsattsaura'.

Gabannin yanke hukuncin, kungiyar kare hakkin bil adam ta 'Human Rights Watch', ta yi kira ga kasar, da a saki mutanen, inda ta ke cewa, "Hukuncin zai kara sa fargaba a tsakanin masu fafutukar kare 'yan luwadi da madugo, ba wai a Aceh kawai ba har ma da wasu wuraren da dama, musamman a lardunan masu 'tsattsauran' ra'ayi na kasar.

Za a yi wa mutanen bulala a lokacin da za a gudanar da wani biki a ranar 23 ga watan Mayu, a lardin birnin Banda Aceh, inda masu sintiri suka kama su.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce, kyamar luwadi na karuwa a kasar.

Tun sama da shekara goma da ta gabata, aka bai wa lardin Aceh dama ta musamman don gabatar da dokokin shari'ar Musulunci nata na kanta.

Labarai masu alaka