Shugaban Bundu dia Kongo ya gudu daga gidan yarin Kinshasa

DR Congo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayan shugaba Ne Muanda Nsemi sun kai wa gidan yari hari a Kinshasa

Mai magana da yawun gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ya ce mabiyan kungiyar addini da siyasa sun kutsa cikin kurkukun da ke birnin Kinshasha , inda suka saki shugabansu da fursunoni 50.

An ji harbin bindiga a gidan yarin yayin da Ne Muanda Nsemi da wasu fursunonin suka tsere.

'Yan sanda na zaton sun harbe fursunoni da dama.

Mista Nsemi shi ne shugaban kunigiyar da ke kokarin farfado da matsarautar Kongo.

An dai kama mista Nsemi tare da matansa uku da dansa daya a watan Maris, bayan wani rikici tsakanin magoya bayansa da 'yan sanda.

Nsemi wanda yake ikrarin annabta sannan kuma shugaban haramtacciyar kungiyar ta Bundu dia Kongo ke son farfado da tsohuwar masarautar yankinsu .

Mista Nsemi dai na son ganin ya dawo da daular da yake hankoron kafawa a sassan jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Congo-Brazzaville da Angola da kuma Gabon.

shugaban kungiyar ya kasance dan majalisar Kinshasha a lokacin da 'yan sanda suka kama shi.

Mai magana da yawun gwamnati, Lambert Mende ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa ''Magoya bayan Bundu Dia Kongo sun kai hari a gidan yarin Makala da alfijir, inda fursunoni 50 da shugabansu Ne Muanda Nsemi suka tsere.''

Wakilin BBC Mbelechi Msosh ya ce ana shirin sake kama fursunonin da suka arce a Kinshasa.

Jami'an ba da agaji na Red Cross na kai gawawwakin fursunoni da dama dakin adana gawa a asibitoci daban-daban.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce gidajen yarin kasar na da cinkoso kuma babu tsaro mai inganci.

Karin bayani