Ina nan daram a Tottenham: Pochettino

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pochettino ya sanya hannu a karin kwantiragi a watan Mayun 2016

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya musanta rahotannin da ke cewa zai bar kungiyar, yana mai jaddada cewa yana nan daram a cikinta.

Kocin dan asalin Argentina, mai shekara 45, ya koma Tottenham ne daga Southampton a watan Mayun 2014 a kan kwantiragin shekara biyar.

A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, ya kara sanya hannu a karin kwantiraginsa da kungiyar har zuwa 2021.

Ya ce: "Akwai jita-jita da yawa, amma ni ina jin dadin zamana a kungiyar."

Ya kara da cewa : ''Ba wani dalili da zai sa ni barin kungiyar. Ina nan daram a kungiyar domin a kwantiragina babu wata dama ta barin kungiyar idan na so. Ina nan har kakar wasa ta gaba.''

Labarai masu alaka