Shugaban Sudan zai gana da Trump a Saudiyya

Omar El Bashir Hakkin mallakar hoto STR/AFP/GETTY IMAGES
Image caption Ana tuhumar El Bashir da laifuka yaki

Kasar Saudiyya ta gayyaci shugaban Sudan Omar al-Bashir, wanda kotun duniya ke nema ruwa a jallo, saboda aikata laifukan yaki, zuwa wani taro da za a yi da shugaban Amurka Donald Trump, da Larabawa, da Musulmai.

Har yanzu dai shugaban bai ce komai ba a kan wannan gayyatar da aka yi masa.

Mista Trump zai kai ziyara kasar ta Saudiyya daga ranar Asabar, a ziyararsa ta farko zuwa kasar tun bayan hawansa kan karagar mulki.

An shirya shugaban na Amurka zai yi jawabi a taron, "a fatansa na zaman lafiya tare da Musulunci".

A shekarun 2009 da 2010, kotun hukunta manyan laifuka ta bayar da sammacin kama Mista Bashir, saboda laifin kisan kare dangi, da laifukan yaki, da kuma laifukan da suka shafi cin zarafin dan Adam da ke da alaka da rikicin Dafur, inda aka kashe rayuka 300,000.

Ya dai musanta zarge-zargen, ya kuma samu nasarar tsallake wa kamun da ake son yi masa a shekaru da yawa.

Labarai masu alaka