Kun san Muzurun da ya fi ko wanne tsayi a duniya?

Stephy da Omar Hakkin mallakar hoto @OMAR_MAINECOON
Image caption Omar ne muzurun da ake kyautata zaton ya fi kowane mage girma a duniya

A lokacin da Stephy Hirst ta dauki muzurun mai suna Omar ta tafi da shi gida, girmansa daidai yake da jariran kyanwoyi.

Amma yanzu muzurun wanda aka dauka daga Australia mai tsayin santimita 120 zai iya kasancewa mage mafi girma da tsayi a duniya.

Bayan katon muzurun ya yi suna a intanet, Ms Hirst ta ce mujallar Guinness World Record wdnda ke tara bayanan abubuwan al'ajabi na duniya suka tuntube ta suka ce ta aika musu da tsayin muzurun.

Neman suna

Ms Hirst ta bude wa Omar shafi, a shafin sada zumunta da muhawara na mako biyu, kuma mutane sun aika sakonni sama da 270,000 a shafinsa.

Tuni aka yada hotunan muzurun a jaridun Australia da ma gidajen talabijin din kasar.

Omar na tashi ne da misalin karfe 5 na safe, sai ya dan ci abinci kadan a matsayin karin kumallo sai ya dan yi yawace-yawacensa sai kuma ya ci danyen naman dabbar Kangaroo a matsayin abincin darensa.

Muzurun wanda girmansa ya fi sauran maguna, yana zubar da gashinsa ko ina cikin gida.

Muzurun mai nauyin kilogram 14, ba shi da kuzarin yin abubuwa. Sai da da abin daukar kare take daukar sa ta kai shi wajen likitan dabbobi saboda girmansa.

Omar na iya bude kofofin gidan da kwabet din kitchen da na dakuna.

Hakkin mallakar hoto @OMAR_MAINECOON
Image caption Muzurun ya fi so ya rika zamansa a gida ba tare da ana zuwa ganin sa ba

Mis Hirst ta ce, "Duk kawayenmu da abokamu naso su zo su ga muzurun." Ba su amince da hotunansa da nake sakawa a intanet ba, sun zaci hoton karya ne. Sai da suka ganshi a zahiri suka rika mamaki."

Da zarar mujallar Guinnes World Record ta samu shaidar abin al'ajabi, zai iya daukar tsawon makonni 12 kafin ta mayar da martani.

Masu wakiltar Australia ba su tabbatar da matsayin bukatar da Mis Hirst ta shigar ba amma ba wai damuwa ta yi da sunan da zai yi ba.

Saboda a ganinta, Omar ba zai so yin suna ba, zai fi so ya koma rayuwar da ya saba ta zama cikin gida ba tare da ana ganin sa ba.

"Kawai ya fi so ya yi kwanciyarai a cikin gadon da yake kwantawa yana cin naman dabbar Kangaroo sannan kuma ya hana mu bacci da daddare," a cewarta.

" Ina ga dai zai fi so ya zama kamar sauran maguna a gidaje.

Labarai masu alaka