Wata mata ta haihu a mota kirar bas a Lagos

Birnin Legas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dandazon mutane ne suka taru suna leke domin ganin abin da ke faruwa cikin bas din

Kafofin yada labarai na ta yada bidiyon wata mata da ta haihu a cikin wata motar bas a birnin Legas da ke Najeriya.

Bidiyon ya nuna dandazon mutane da ke leke cikin motar bas din a wurin da motocin haya ke tsayawa a unguwar Fayedi.

Bayan 'yan dakikoki sai aka fito da wani jariri wanda bisa ga dukkan alamu a lokacin aka haife shi, daga cikin motar, sannan aka shiga da shi wata motar daukar marassa lafiya.

Bayan an yi haihuwar, sai aka fito da wata mata wacce alamu suka nuna ita ce mahaifiyar dan daga cikin bas din, aka shige da ita cikin motar daukar marassa lafiyar ita ma, yayin da dandazon mutanen ke ta shewa suna kuma daukar hotuna da wayoyinsu.

Bidiyon ya bayyana a wurare daban-daban a cikin kwanakin da suka gabata.

Duk da haka, wani mai magana da yawun kamfanin Rapid Bus Service ya shaida wa Sashen BBC Africa Live Page cewa lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Afrilu kuma sun kasa gano inda matar take.