An nada wanda zai binciki Rasha kan zaben Trump

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robert Mueller, tsohon mai gabatra da kara ne wanda ya yi aiki a matsayin shugaban FBI tsakanin shekarar 2001 da 2013.

Ma'aikatar sharia'ar Amurka ta yi shelar nada mai gabatar da kara na musamman wanda zai yi bincike kan zargin cewar Rasha ta tsoma baki a zaben shugaban kasan Amurka da aka yi bara.

Wanda ma'aikatar ta nada shi ne tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Rober Mueller.

A sanarwar da ta fitar domin nada tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Rober Mueller, a matsayin mai gabatar da kara na musamman da zai jagoranci bincike kan zargin da aka yi wa Rasha cewar ta tsoma baki a zaben shugaban kasar Amurkan bara, ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce nada wani mutum mai zaman kansa ya jagoranci binciken abu ne da ya dace da muradun Amurkawa.

Sanarwar na zuwa ne bayan ce-ce-kucen da ya kaure a Washington lokacin da Shugaba Trump ya sallami mutumin da yake jagorancin binciken a baya, shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, James Comey.

Hukumar FBI da majalisar dokokin murka na bincike kan yiwuwar samun alaka tsakanin kungiyar yakin neman zaben Trump da Rasha.

Hukumomin leken asirin Amurka sun yi ammanar cewar Moscow ta yi kokarin karkata zaben ta hanyar dan Republikan din.

'Yan siyasa daga bangarorin biyu sun yi maraba da sanarwar nada Robert Mueller, a matsayun wanda zai jagoranci binciken.

Jim Himes dan majalisar dokokin Amurka ne.

"Na ji dadin hakan matuka. Na farko cewa an nada shi. Na biyu cewar Bob Mueller wanda jarumi ne wanda ba za a iya tantama kan mutuncinsa ba. Saboda haka na yi farin cikin ganin hakan."

Mr Mueller, mai shekara 72, ya yi aiki a matsayin darakatan hukumar FBI na tsawon shekara 12 a karkashin Shugaba George W Bush da Shugaba Barack Obama, kuma ya fi kowa dadewa a shugabancin hukumar tun zamanin, shugaban hukumar na farko, John Edgar Hoover.

Ana tsammanin zai yi murabus daga wani ofishin aikin lauya mai zaman kansa domin kauce wa cin karon muradunsa da na kasa.