Yadda wata 'yar Chibok ta tsere daga hannun Boko Haram

'Yan matan Chibok 82 aka ceto ranar 6 ga watan Mayu
Image caption 'Yan matan Chibok 82 aka ceto ranar 6 ga watan Mayu

Gwamnatin Najeriya ta ce wata yarinya daga cikin 'yan matan Chibok da suka rage a hannun kungiyar Boko Haram ta tsere daga hannun kungiyar.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ne ya tabbatar wa da BBC hakan, inda mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a wajen taron majalisar minsitoci a ranar Laraba.

An yi amannar cewa wasu sojoji ne suka tsince ta a lokacin da tsere tana hanyar guduwa.

Mista Adesina ya kara da cewa sai dai kuma ba a yi wani karin bayani kan ko wacece ita ba, ba kuma a fadi a halin daaka tsince ta ba.

Kun san 'yan Chibok ɗin da suka ƙi yarda su koma gida?

Na fi son zama a hannun Boko Haram— 'Yar Chibok

Kun san 'yan matan Chibok din da aka ceto?

A ranar 6 ga watan Mayu ne kungiyar Boko Haram ta sako 'yan mata 82 na makarantar sakandaren Chibok din, bayan sasantawar shiga tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram din da wasu kungiyoyi da kasashe suka yi.

Labarai masu alaka