Nigeria: Cin hanci na dakile yaki da Boko Haram—TI

Rundunar sojin Nigeria ta sha nanata cewa tana hukunta duk wasu jami'anta da aka samu da aikata laifi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin Nigeria ta sha nanata cewa tana hukunta duk wasu jami'anta da aka samu da aikata laifi

Kungiyar Transparency International TI ta ce cin hancin da rashawan da ake tafkawa a tsakanin sojojin Najeriya na dakile kokarin da kasar ke yi na yaki 'yan kungiyar Boko Haram.

Kungiyar ta zargi jami'an sojin da kirkirar kwangiloli na bogi da kuma kakatar da kudade da nufin samar da kayayyakin aikin da ake bukata.

Transparency International ta ce hakan na kawo cikas ga kokarin da ake na murkushe masu tayar da kayar bayan.

To sai dai mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar, Manjo janar John Enenche, ya ce wadannan zarge-zarge sam ba su da tushe a tsakanin jami'an su.