Za a binciki yadda 'yan sanda suka 'gallazawa' wani mutum

An yada bidiyon a shafukan sada zumunta Hakkin mallakar hoto Youtube screengrab
Image caption An yada bidiyon a shafukan sada zumunta

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta mayar da martani a kan wani bidiyo da yake nuna 'yan sanda a birnin Benin na jihar Edo da ke kudancin Najeriya suna jan wani mutum a kasa da motarsu, inda suka daure hannunsa da ankwa a jikin motar.

Wani dan kallo ne ya dauki bidiyon, mai tsawon minti 1:34, da wayarsa ta salula, kuma an yi ta yada bidiyon tamkar wutar daji a kafofin sadarwa na zamani kamar Facebook da YouTube.

A sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar ta ce, tuni ta kaddamar da bincike don gano ainihin abin da ya faru a ranar Lahadi 14 ga watan Mayu.

Sai dai sanarwar rundunar ta ce, ko a cikin bidiyon ba a nuna inda motar take jan mutumin ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Rundunar ta kuma ce 'yan sandan suna bakin aiki ne a lokacin bayan da suka sami rahoton wasu 'yan kungiyar asiri za su aikata laifi, inda suka samu nasarar kama mutane biyu, sauran kuma sun

Mai kama da Messi ya shiga hannun 'yan sanda a Iran

'Yan sanda su yi mana bayani kan kisan Sheikh Jaafar'

An yi arangama tsakanin soji da 'yan sanda a Yobe

Sanarwar ta kuma ce mutumin ya yi kokarin tserewa ne bayan da mutanen wata anguwa suka hana 'yan sanda wucewa da wadanda suka kama.

Wannan lamari dai ya tayar da hankalin jama'a da suka kalli bidiyon.

A cikin bidiyon ana iya jin muryar wani yana cewa, "wannan ai rashin imani ne, rashin tausayi ne", wani kuma yana cewa "wai me ya yi ne?, dubi bakinsa har kumfa na fitowa".

Hakkin mallakar hoto Youtube screengrab
Image caption Police

Labarai masu alaka