Turkiyya ta gina wa marayun Syria sabon birni

Yara 18 ne za su zauna a ko wanne gida da ke birnin Hakkin mallakar hoto ORPHANS CITY
Image caption Yara 18 ne za su zauna a ko wanne gida da ke birnin

Kasar Turkiyya, ta bude babbar cibiyar da ta sadaukar aka gina gidaje da makarantu ga wadanda yakin kasar Siriya ya rutsa da su.

Sabon birnin yana kudu maso gabashin iyakar birnin Reyhanli, inda zai dauki yara 990, abin da kafar watsa labaran kasar ta ce, "gina gidajen abin jin dadi ne."

Za a gina gidaje 55, da makarantu hudu, da masallaci, da filin wasan yara da wajen yin wasanni.

An gina cibiyar a cikin kasa da shekara biyu, tare da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da kuma wasu kungiyoyin bayar da agaji guda biyu.

Hukumar kula da asusun kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, rikicin Siriya da aka shafe shekara shida ana yi ya shafi kimanin yara miliyan shida.

Sama da mutum miliyan biyu ne suka kauracewa kasarsu a matsayin 'yan gudun hijira.

Yanzu haka kasar ta karbi bakuncin sama da yara 800,000 na kasar Siriya da suke makaranta, daga cikinsu kashi 60 cikin dari ne kawai suka samu damar fara karatunsu.

An gina birnin marayun ne tare da taimakon gidauniyar bayar da agaji ta gwamnatin Turkiyya IHH, da gidauniyar bayar da agaji ta Sheikh Thani bin Abdullah (RAF) na kasar Qatar.

A shafinsu na intanet sun bayyana cewa, "Manufarsu ita ce su taimakawa marayun da suka shiga cikin halin firgici sakamakon yakin Siriya," musamman wadanda suke kwana a kan tituna.

Yara 18 ne za su zauna a ko wanne gida mai hawan bene biyu tare da mai kula da su, kuma za su yi karatu a makarantun firamare biyu da na sakandire biyu da aka gina a cikin birnin.

Rahotanni sun ce wasu yaran 5,000 da ba su samu damar zama a birnin marayun ba, za su amfana da kayayyakin more rayuwar da ke birnin.

Labarai masu alaka