China: Za a hana cin naman kare a wurin biki

Masu suka sun ce sau da yawa ana sace karnukan da ake zama da su a gida Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu suka sun ce sau da yawa ana sace karnukan da ake zama da su a gida

Masu fafutuka na Amurka sun ce za a haramta sayar da naman kare a wannan shekarar, a wajen yin bikin cin naman kare na kasar China, saboda gallaza musu da ake yi.

Yanzu haka akwai shakku a kan batun, kuma wasu daga cikin masu sayar da karnukan sun shaida wa BBC cewa, su dai ba su ji wani abu game da haramtawar ba.

A kasar ta China cin naman kare ba laifi ba ne, sai dai bikin shekara da za a yi a lardin Guangxi ya sa ana rade-radi a kasar sannan wasu kashashe yin suka.

Masu suka sun ce, sau da yawa ana sace karnukan da ake zama da su a gida ko wadanda suke yin aiki a yi musu kisan gilla.

'Za a haramta'

Kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dabbobi da dama na cewa, an shaida wa masu sayar da karnukan da masu gidajen abinci cewa, ba za a bari a sayar da naman kare ba a lokacin da ake gudanar da bukukuwan wannan shekarar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane na cin naman karen a bikin da aka yi na shekarar da ta gabata

Dokar za ta shafi masu sayar da naman karen, da kuma masu gidajen abinci. Sai dai dokar za ta zama ta wucin gadi ce, abin nufi ana iya kashe karnukan masu yawa gabannin bikin tun da ba a bayar da sanarwa a hukumance ba.

A fadin kasar ana ci gaba da cin naman karen a matsayin al'adar kasar da kuma abincinsu na gargajiya.

Sai dai ana kallon rahoton haramtawar a matsayin wani abin mamaki ga mutanen Yulin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi bandar karnuka

Wani mai shahararren gidan abincin naman kare a birnin ya yi magana da BBC inda yake cewa, "Au haramta sayar da naman kare za a yi?, ni ban san da wannan labarin ba."

"Duk wanda yake son ya ci, zai iya ci gaba da cin abinsa, me yasa naman kare ya bambanta da sauran nama?" in ji shi.

Har ila yau, kananan jami'an gwamnati da dama sun ce, ba su ji wani abu game da haramtawar ba.

Wata mai fafatuka ta kasar Chana wacce ta ke zuwa bikin duk shekara don ta nuna rashin amincewarta, ta shaida wa BBC cewa, ita ma ta ji jita-jitar haramtawar, sai dai ba wanda ya son daga inda aka samo wannan labarin.

A shekarar da ta gabata ma, gwamnati ta haramta kashe karnuka a bainar jama'a, tare da daukan kwakkwaran mataki a kan hakan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karnuka a rataye

Kungiyoyin kare hakkin dabbobi sun fi mayar da hankali a kan zaton da ake yi na satar karnuka a gidaje ko gonaki, inda ake lodasu a motar daukan kaya a kai su arewa maso yammacin kasar, inda naman karen ya fi shahara.

Mista Li ya yi bayanin cewa,"Akwai kimanin karnuka miliyan 150 a kasar, kuma daga cikin kowanne mutum 10 sai an samu mutum daya da yake da kare. Kashi 40 cikin 100 na karnukan ana zama da su ne a matsayin dabbobin gida, kasa da kashi biyar na mutanen kasar ne kawai suke cin naman kare."

Labarai masu alaka