Japan: Za a kori Gimbiya daga fada saboda auren talaka

Gimbiya Mako Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gimbiya Mako ita ce babbar jikar sarki Akihito

Gimbiya Mako, 'yar gidan sarautar Japan, za ta rasa darajarta bayan da ta amince da auren talaka.

Gimbiyar mai shekara 25, wacce jika ce ga Sarki Akihito, za a yi mata baiko da Kei Komuro, wanda karamin ma'akacin wani kamfani ne, bayan da suka hadu a jami'a.

Dokar sarautar Japan dai, ta bukaci gimbiya ta bar cikin iyalan gidan sarki da zarar ta auri talaka.

Lamarin dai zai jawo ce-ce-ku-ce a kan wanda zai gaji Sarkin, wanda ake tsammanin zai yi murabus nan ba da dadewa ba.

Gimbiya Mako da saurayin nata, Kei Komuro sun hadu ne a shekarar 2012 a wani gidan cin abinci, lokacin da suke karatu tare a jami'ar birnin Tokyo.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista komuro ya yi karatu tare da gimbiyar a jami'ar Tokyo

Mai magana da yawun masarautar ya shaida wa gidan rediyon kasar cewa ana shirye-shiryen yi wa Gimbiyar baiko da saurayin nata.

Gidan radiyon kasar ya ce baikon zai kammala ne kawai da zarar an yi musanyar kyaututtuka.

Kafafen yada labarai dai, sun ce ana sa ran yin daurin auren a shekara mai zuwa.

Da aka tambaye shi game da shirin baikon nasu, sai saurayin ya ce, "Yanzu ba zan ce komai ba a kan lamarin, amma zan yi magana idan lokacin ya zo".

Labarai masu alaka