Jarumar Bollywood Reema Lagoo ta rasu

Jarumar Bollywood, wacce ta shahara da fitowa a matsayin "uwa abar kauna", ta mutu tana 'yar shekara 59.
Ta mutu ne ranar Laraba da daddare a asibitin birnin Mumbai bayan ta sha fama da ciwon bugun zuciya.
Tauraruwar sananniya ce wajen taka rawar zama uwa ga jarumai a fina-finai da shirye-shiryen gidajen talabijin.
Ta fito a manyan fina-finan kasar, kamar su Hum Aapke Hain Koun, da Kuch Kuch Hota Hai, da kuma Maine Pyar Kiya.
Lagoo ta fara shirin fim ne a shekarun 1970, kuma nan da nan ta zama sananniyar mai taka rawa a matsayin uwa ga jarumai.
Ana yi mata lakabi da "uwar fim" ga sannanne jarumi Salman Khan, wacce take fitowa a matsayin mahaifiyarsa a mafi yawan fina-finai.
Ta fito a matsayin mahaifiyar Salman Khan a fim dinsa na farko, a shekara 28 da ta gabata, lokacin tana shekara 31.
Mutane na bayyana alhininsu a shafin sada zumunta na twitter.