Me shigar Malamai siyasa ke nufi?

Wasu Malaman Coci sun ce shigar Fasto siyasa ka iya ɓata sunan addininsa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu Malaman Coci sun ce shigar Fasto siyasa ka iya ɓata sunan addininsa

Siyasa, a al'adance, harka ce da ake jinginawa ga masu tsageranci, ƙarya, da rashin cika alƙawari.

Shi ya sa ma a ƙasar Hausa idan mutum ya yi alƙawari bai cika ba sai a ce masa ɗan siyasa.

Ko a ƙasashen da aka ci gaba, irinsu Amurka da Burtaniya, idan 'yan siyasa suka tashi yaƙin neman zaɓe, kalamansu cike suke da kakkausar suka da cin mutunci.

Hakan ya faru a baya-bayan nan lokacin da aka fafata tsakanin tsohuwar Sakatariyar wajen Amurka Hillary Clinton da abokin hamayyarta wanda kuma shi ne shugaban ƙasa Donald Trump.

Sun yi ta yin kalamai na cin mutunci, abin da ke nuna irin yanayin da harkokin siyasa ke ciki hatta a kasashen da suka yanke wa dimokradiyya cibiya.

Shi ya sa a kwanakin baya da Shugaba Trump ya sanya hannu a kan wata doka da za ta bai wa Malaman addinai damar shiga harkokin siyasa aka aza ayar tambaya: Shin ya dace Malaman su shiga a dama da su a cikin wannan harka da ba a ganin kowa da gashi, musammam a ƙasashe kamar Najeriya da Jamhuriyar Nijar?

Da dama daga cikin mutane na ganin shigar Malaman addinai cikin siyasa zai sa a samu tsafta kan yadda ake gudanar da mulki da kuma ita kanta siyasar.

Masu irin wannan ra'ayi na ganin cewa Malaman za su yi amfani da ilminsu na addini, wanda ke jaddada bukatar yin adalci ga kowa da kowa, wajen tafiyar da harkokin jama'a - abin da ake zargin 'yan siyasa da kaucewa.

Sheikh Musa Sani, wani Malami ne a Abuja kuma ya gaya min cewa shigar Malamai harkokin siyasa yana da matukar alfanu.

"Ya kamata Malamai su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa saboda al'amari ne da ya shafi al'umma gaba daya. Wasu na cewa tsarin siyasarmu ba na addini ba ne amma ya kamata su yi la'akari cewa wannan tsarin yana da tasiri kan addininmu don haka dole su sanya baki a cikinsa ta yadda za su sauya shi ya dace da addini maimakon su bari marasa ilimi su rika jagorantarsu," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu na ganin ya kamata malamai su shiga a dama da su a harkokin siyasa

'Zai ɓata sunan addini'

Sai dai ba duk aka taru aka zama ɗaya ba: Wasu na ganin shigar Malamai harkokin siyasa zai zubar musu da mutunci sannan ya sa al'umma ta daina martaba ilmin da suke da shi.

Sakatare Janar na kungiyar CAN ta Najeriya, Musa Asake, ya gaya min cewa bai kamata Malaman addini su shiga siyasa ba, sai sun sauka daga kan mukamin da suke rike da shi a addinance domin gudun ɓatawa addini suna.

Ya ce "A baya ana hana Malaman Coci-Coci shiga siyasa saboda zage-zage da cin mutuncin da ke cikinta, amma yanzu mun ce duk wani mai rike da mukami a Coci ya sauka daga mukamin ya shiga siyasa, saboda akwai 'yan jam'iyyu daban-daban a cikin Addini. Kuma idan ya shiga ya ɓaci, maimakon a ce Fasto, to an san yanzu ya zama dan siyasa."

Ko yaya batun yake a mahangar masana harkokin siyasa?

Dr Sa'idu Ahmad Dukawa, wani Malami ne a Sashen nazarin harkokin siyasa na Jami'ar Bayero da ke Kano, kuma shi ma ya shaida min cewa dole Malamai su shiga siyasa idan suna so a samu ci gaba.

A cewarsa, "A fahimtarmu ba a raba addini da siyasa. Hasalima, idan ka fassara siyasa da shugabanci, dukkan annabawa 'yan siyasa ne. Da ma Allah ya ce zai halicci khalifa a ban kasa, don haka mu a ganinmu siyasa da addini tamkar Danjuma ne da Dan Jummai".

Malamin Jami'ar ya kara da cewa wasu jahilai ne suka ɓata siyasa saboda da son zuciya, sai duk wani mai martaba da mutunci ya ja da baya "amma dole masu mutunci su koma fagen siyasa idan ana so kasashe irin namu su ci gaba".

"Ko su shiga ko kar su shiga sai siyasa ta yi tasiri a kansu. Kar ka manta cewa da ita ake yin dokar da za ta sa ko hana Malami ya yi wa'azi ko ma gudanar da addininsa. Don haka wajibi ne su shiga siyasa", in ji Dr Sa'idu Ahmad Dukawa.

Da alama dai bangarorin biyu za su ci gaba da fafutukar kare matsayinsu bisa la'akari da hujjojin da suka bayar.

Sai dai masana na ganin ko mai daren dadewa wani bangaren zai rinjayi dayan idan aka yi la'akari da sauye-sauyen da ake samu a duniya cikin harkokin siyasa.

Labarai masu alaka