Mukaddashin shugaban Najeriya ya karbi kudurin kasafin kudi na 2017

Ofishin mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi kudirin dokar kasafin kudin shakara ta 2017 na Naira tiriliyon 7.44, in ji wani jam'in gwamnati ranar Jumma'ah.

Kakakin mukaddashin shugaban kasar Laolu Akande ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa "Ofishin mukaddashin shugaban kasa ya karbi kudirin dokar kasafin kudin shakara ta 2017, kuma za a sanya masa hannu bayan an bi dukkan ka'idodjin da suka kamata".

Shi ma Sanata Ita Enang, babban mai ba shugaban kasa shawara a kan dangataka da majalisar dattawa ya ce kasafin na bana zai taimaka wajen fitar da Najeriya daga matsalar tattalin arzikin da take fama da shi - kuma mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai rattaba hannu.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ta amince da kasafin kudin .

Kasar - mai karfin arzikin man fetur - tana cikin shekara ta biyu ta koma bayan tattalin arziki, wanda karyewar farashin mai ya janyo ya jawo raguwar kudaden shiga a baitulmalin gwamnati.

Lamarin kuma ya shafi karancin kudaden waje kamar dalar Amurka, kana ya raunata karfin naira.

Dole shugaban kasa ya sa hannu kafin kasafin kudin kafin ya zama doka.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari yana kasar Birtaniya inda yake yin jinya

Shugaba Muhammadu Buhari yana kasar Birtaniya inda yake yin jinya, kuma ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Osinbajo, wanda shi ne zai rattaba hannu a kan kudirin dokar.

"Bayan na mika kudurin kasafin kudin ga mukaddashin shugaban kasar, ya ce zai rattaba hannu bayan an bi dukkan ka'idojin da dokar kasa ta tanadar", in ji Enang, lokacin wata ganawa da yayi da 'yan jarida a Abuja, bayan ya fito daga ganawa da Farfesa Osinbajo.

Kasafin kudin bara -- wanda aka sanya ma hannu a watan Mayun 2016 -- ya sami jinkirin watanni saboda takardamar da ta taso tsakanin 'yan majalisa da bangaren zartaswa na shugaban kasa, lamarin da ya dakatar da sakin kudaden tafiyar da ayyukan gwamnati; kuma ya jawo koma baya ga tattalin arzikin kasar.

'Yan majalisa sun lashi takobin kammala aikin kasafin kudin bana a kan lokaci domin gudun maimaicin lamarin a bana.

Duka majalisun kasar guda biyu sun amince da su kara yawan kasafin kudin, wanda ya zarce wanda shugaba Buhariya tura musu na Naira tiriliyan 7.298 a watan Disamba.

An shirya kasafin na bana bisa farashin mai na dalar Amurka 44.50 kan kowace gangar mai, duk da cewa farashin mai na Brent ya zarce dala 50 a kasuwannin duniya. Kasafin kuma ya ware Naira tiriliyan 1.488 domin biyan basusukan kasashen waje da na cikin gida.

Labarai masu alaka