Guguwa mai karfi ta kashe mutum uku a Sokoto

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Hakkin mallakar hoto Imam Imam
Image caption Mutum uku ne akalla suka rasa rayukansu a Jihar Sokoto ta arewacin Najeriya

Wata guguwa mai karfin gaske ta kashe mutum uku a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

Jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, NEMA,Suleiman Muhammed mai kula da jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi ne ya bayyana haka.

Ya ce lamarin ya auku ne ranar hudu ga watan Mayu na bana, inda guguwar ta ruguza gidaje fiye da gida 1,000 a kananan hukumomin Shagari da Tambuwal.

Jimillar gidaje sama da 1,000 sun rushe a kananan hukumomin Anka da Maradun da Birnin Magaji. Daga watan karshen watan Afrilu na bana zuwa yanzu, guguwar ta shafi jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara.

"Idan annoba ta faru, da farko zamu je mu tabbatar da tsaro a gurin, kuma mu kididdige yawan barnar, sannan mu rubuta rahoton irin taimakon da suke bukata", in ji jami'in.

Guguwar ta haifar da asarar dukiya mai yawa.

Suleiman Mohammed ya ce "Idan aka kiyasta abin da shafi Sokoto da Zamfara ya kai sama da miliyan 100 na Naira.''

Jami'in ya bayar da shawarar hanyoyin magance aikuwar irin wannan lamarin nan gaba, inda ya ce "Shuka itatuwa zai taimaka wajen rage asara irin wannan nan gaba".

Labarai masu alaka