Maciji ya sari mutumin da zai sumbace shi

maciji Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi amannar macijin ya gudu bayan ya harbe shi

Wani mutumin Florida ta Amurka ya fara farfadowa a asibiti bayan da ya gwada sumbatar maciji amma sai macijin ya sare shi, inda aka garzaya da shi asibiti.

A ranar Litinin ne Charles Goff wani mazaunin yankin Putman da ke arewa maso gabashin yankin Putnam ya samo macijin.

Kwana daya bayan ya samo macijin, wani makwabcinsa wanda wata kafar yadda labarai ta CBC ta kira Ron Reinold, ya fara wasa da macijin kuma ya yi kokarin sumbatar macijin.

Jirgin sama ne ya dauke shi zuwa asibiti kuma a yanzu haka yana farfadowa.

Mista Goff ya shaidawa kafar yada labarai ta Action News Jax cewa, "Wannan yaro ya ce zai sumbace shi a baki, sai macijin ya harbe shi a fuskarsa."

Ya kara da cewa, "Wauta ce kurum irin ta Ron, ka gane? Ina ga cewa ya yi zai iya sumbatar macijin kuma babu abin da zai same shi, amma kuma sai aka samu akasin haka.

Kafar yada labarai ta First Coast News ta ce mutumin na cikin hayyacinsa amma kuma da farko yana cikin mummunan yanayi.

An yi amannar macijin ya gudu bayan ya sari mutumin.

Har yanzu dai ba a tabatar da abin da yasa Mista Reinold ya yi kokarin sumbatar macijin ba.

Labarai masu alaka