Nigeria: Sojoji sun far wa tsagerun Niger Delta

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga tsagerun yankin Naija Delta su daina fasa bututan mai ko ta murkushe su. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga tsagerun yankin Naija Delta su daina fasa bututan mai ko ta murkushe su.

A Najeriya, rundunar tsaro a yankin Naija Delta ta ce ta bankado maboyar masu satar mutane don neman kudin fansa da kuma fashi a teku a wani samame da dakarunta suka kai a yankin.

Rundunar ta ce dakarunta sun yi nasarar kubutar da mutane biyu tare da kwace manya da kananan makamai.

Mai magana da yawun rundunar 'Operation Delta Safe' Manjo Abubakar Abdullahi, ya shaida wa BBC cewa sun kai samamen ne bayan samun wasu muhimman bayanai da aka kwarmata musu.

Ya ce, "Da dama daga cikin barayin sun ji rauni sakamakon harbin bindiga da aka musu, inda wasun su suka fada a cikin ruwa, wasu kuma sun tsere da raunin harbin bindiga."

Satar mutane ana garkuwa da su don neman kudin fansa da fashi a teku, wasu tagwayen matsaloli ne da ke ci gaba da addabar yankin Naija Delta na kudancin kasar.

Labarai masu alaka